Ya Nemi Al\’ummar Musulmi Da Su Kula Da Tarbiyyar \’Ya\’yansu

0
965

Zubair A Sada, Daga Kaduna

BABBAN Limamin sanannen masallacin Juma\’a da ake wa lakabi ko kiransa da sunan Masallacin Juma\’a na Danfodiyo, da ke Unguwar Sanusi, Kaduna; Sheikh Abdulhadi Aliyu Daura ya nemi al\’ummar Musulmi da su ji tsoron Allah kuma su yi masa da\’a tare da yin da\’a da ma kwaikwayon Manzon Allah da bibiyar magabata su dinga neman hanyoyin da za su bi domin yi wa \’ya\’yansu tarbiyya ta kwarai wadda ta dace da addinin Musulunci.

Sheikh abdulhadi Daura ya ce, tarbiyyar \’ya\’yanmu wajibi ce a kan kowane magidanci musamman ma kuma uba wanda ya haifi dan ko \’ya. Ya ce, dole ne mu ladabtar da yaran da Allah ya ba mu, domin Allah zai tambaye mu a gobe kiyama. Sai ya kara da cewa, tarbiyyar diya mace ta fi hadari kan na da namiji, domin shi da namiji kana iya dora shi kan irin sana\’ar da kake yi, idan za ka tafi kasuwa ne ku tafi tare da sauransu; amma diya mace idan ka tafi ka barta, to, hadisin nan da yake maganar kadaita mutum biyu, na ukun su shaidan ne shi ne abin da ke faruwa a halin yanzu.

Malamin a cikin hudubarsa na sallah babba, ya ce, \’\’wannan babbar rana ce mai daraja, Manzon Allah ya kirata da \’\’yaumil hajji akbar\’\’. 11 ga wata, kuma ranar Juma\’a, babu abin da ya fi soyuwa fiye da yankan na a wurin Allah, wato zubar da jinaina na dabbobin ni\’ima. kain ma jinin ya kai kasa, Allah ya karbi ayyukan mutum kuma ya gafarta masa muddin an yi shi domin neman yardar Allah ne. Dabbar nan kuma za ta zo ranar alkiyama domin ceton mutum kamar yadda ya zo a wani hadisi\’\’.

Shehin malamin daga nan ya hori jama\’a da su girmama wannan ranar salla babba ta hanyar yin abubuwan da suka dace da amsuwa ga Allah, kamar zikirora da ziyarce-ziyarce da sadaka da hafiya da kyauta da makamantan ayyukan alheri da yawan gaske.

Masallacin Danfodiyi kusan shi ne masallaci na biyu bayan Sultan Bello na Unguwar Sarki, Kaduna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here