Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
A wata tattaunawa ta musamman da GTK ta yi da shugaban hadakar
\’yan kasuwa na karamar hukumar Damaturu cikin Jihar Yobe Alhaji Garba
Bazam akwanakin baya.
shugaban ya bayyana irin halin da mambobin kungiyar suka shiga na
sukurkucewar harkokin kasuwancinsu sakamakon tabarbarewar harkokin
tsaro da yankinsu ya yi fama da shi da yadda gwamnatin jahar ta yi ta
kokarin dafa musu don fita daga wannan halin kunci. Asha karatu
lafiya.
GTK:- Yaya tarihin wannan kungiya ta ku yake da kuma adadin mambobin ku?
Bazam:- To ita wannan hadakar kungiya ta mu ta hadakar \’yan kasuwar
garin Damaturu mun kafa ta ne fiye da shekaru goma da suka gabata.
Kuma a yanzu haka muna da akalla mambobi fiye da dubu 10 wadanda suke
cikin kudinmu.
GTK:- Mambobin kungiyar nan ta ku ta \’yan kasuwar garin Damaturu
sun hadu da iftila\’i iri-iri a \’yan shekarun nan a dalilin
tabarbarewar harkokin tsaro ko yaya abin yake ne?
Bazam:- Lalle kan mambobin wannan kungiya ta mu sun hadu da iftila\’i
daga Allah SWT kashi dabam-dabam tun daga abin da ya kama ga konewar
dukiya sanadiyyar tashin gobara ya zuwa konewar dukiya sakamakon
hare-haren \’yan bindiga da ya kai ga asarar rayuka da dukiyar milyoyin
Nairori. Da kuma karayar tattalin arziki da wannan lamari ya haifar wa
aksarin \’yan kasuwar.
Har ila yau wannan iftila\’i na tabarbarewar harkokin tsaro ya haifar
da mummunan koma baya ga harkokin kasuwancin wannan yanki namu ta
yadda za ka tarar a \’yan shekarun baya mutum daya kan sauke kaya fiye
da tirela 3 a duk sati amma sai da ta kai da lamura suka yi tsamari da
kyar za ka sayar da buhuna 10 kacal a sati. To ai kaga mun ga iftila\’i
iri-iri.
GTK:- To yanzu fa yaya abin yake in ka kwatanta shi da kamar shekaru
uku da suka shude?
Bazam:- A hakikanin gaskiya yanzu kan alhamdulilah da yake an samu
yanayin tsaro ya kyautatu matuka kuma aksarin mutanen da suka
bar garin tunin sun dawo.
GTK:- Ko akwai wani tallafi da gwamnatin Jihar Yobe ta baku sakamakon
wannan iftila\’i iri-iri da ka ce ya fada wa mambobinku?
Bazam:- Alal hakika gwamnatin jahar Yobe karkashin mai girma gwamna
Alhaji Ibrahim Gaidam ta yi matukar tallafa wa mambobin mu domin kuwa
akwai lokacin da aka yi gobaraa cikin babbar tashar motar Damaturu
yadda mambobinmu suka yi asarar shagunansu da dukiyoyinsu amma da
Gwamnan ya zo ya gani sai ya bada umarni da a kiyasta asarar da kowane
dan kasuwa ya yi, da muka yi kiyasi muka kai ma sa cikin kwanaki hudu
kacal ya amince da a biya mu kashi dari bisa dari na dukkanin kiyasin
da aka kai masa yadda ya umarci hukumar kai daukin gaggawa ta jahar
SEMA da ta ba mu Naira Miliyan18 don rarraba wa ga \’yan kasuwar da suka
yi asarar dukiyoyinsu.
Haka nan a wancan lokacin ma da mambobin mu suka hadu da iftila\’in
hare-haren 1` ga watan Disambar 2014 yadda shaguna kusan 78 suka kone
bayan da gwamna ya zo ya gani da idonsa tare da jajanta wa da kuma
wasu wurare akalla 5 da suka hadu da gobara nan ma gwamnan bai yi kasa
a gwiwa ba ya amince da bamu tallafin kudade sama da Naira Miliyamn 60
don rarraba wa wadanda suka samu kan su cikin wannan iftila\’i.
Don haka babu abin da zamu cewa gwamnatin jahar ta Yobe da gwamna
Ibrahim Gaidam sai dai fatan alheri domin kuwa alama ce mai nuna kan
cewar lalle gwamnan na tare da jama\’arsa kana yana kuma tausa wa musu.
GTK:- Ko bayan haka kuna da wani koke ko korafi ga gwamnatin jaha
da kuma ta tarayya dangane da wasu bukatunku?
Bazam:- Ba shakka lalle shi da baya gajiya da kuka ga mahaifinsa duk
irin taimakon da ya ba shi hakika kungiyar mu tana sake neman taimako
daga gwamnatin jahar Yobe dangane da bada jari ga \’yan kasuwar da suka
karye sanadiyyar tabarbarewar tsaron da yankin ya yi fama da shi
kasancewar aksarin \’yan kasuwa rashin ishasshen jari na ci musu tuwo a
kwarya, kuma jarin ko da rance ne da ba shi da ruwa mai yawa
muna bukatarsa.
Haka nan gwamnatin tarayya ma muna rokon ta da ta kawo mana dauki ko
da yake ma dama muna tsammanin hakan daga sabon shugaban mu mai adalci
Muhammadu Buhari kasancewar a kullum tun daga hawansa karagar mulki ya
ke bayanin cewar zai mayar da aksarin akalarsa ga wannan yanki namu
kuma ko yanzu mun gani a kasa tunda tunin ya mayar karfin tsaron kasa
ga wannan yanki namu don kokarin dawo mana da yanayin tsaro mai
inganci.
GTK:- Allah ya taimaka.
Bazam:- Madallah na gode Allah ya albarakaci wannan jarida tamu mai
dadadden tarihi wato GTK.