Sani Gazas Chinade, DAGA DAMATURU
AN bayyana cewar hadin kan al\’ummar musulmi ya zama wajibi musamman a
wannan lokaci da musulmai suka zama tamfar mikiya cikin tsuntsaye a tsakankanin yahudu
da nasara.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Ustas Baba gana Malam Kyari
daya daga cikin Limaman Jumu\’a da Idi a tattaunawarsa da GTK a
garin Damaturu dangane da yadda rashin hadin kan al\’ummar musulmai ke
kawo koma-baya ga al\’ummar ta musulmai wadda hakan ke bada dama ga
yahudu da nasara na yin hawan kawara ga musulman duniya duk da cewar
komai nisan jifa kasa zai fado.
Malamin addinin musulunci ya ci gaba da cewar, ya zama wajibi al\’ummar
ta musulmai su hada kan su in har suna son nasara ta ci gaba da
tabbata a gare su domin kuwa ko a cikin Littafin Alkur\’ani mai girma
Allah (SWT) na cewa mu yi riko da igiyar Allah kar mu rarraba don
rarraba ba abin da za ta haifar mana sai hasara duniya da lahira. Don
haka hadin kai shi ne babban tushen ci gaban al\’umma.
Ustas Baba Gana Malam Kiyari ya ci gaba da cewar, akwai bukatar
wannan hadin kai ya somo daga Malamai jagororin al\’umma domin kowane
malami na da mabiyan da ya ke jagoranta matukar malaman sun hada kansu
to hadin kan mabiya ba zai yi wuya ba. Domin kamar mu anan garin
Damaturu kusan dukannin bangarorin malamai kanmu a hade yake ta
yadda duk abin da ya taso ga daya daga cikin bangarorin mabiya akan
hadu baki ya zo daya don magana da murya daya babu zancen wannan ko
wancan dan kungiya kaza da kaza ne.
Da GTK ke tambayar malamin yadda za a yi a hada kan sai ya amsa da
cewar, a lokacin da mai girma shugaban kasar Nijeriya na yanzu
Muhammadu Buhari ke yakin neman zabe ya ce duk da yadda kasa ta
tabarbare amma in an zabe shi zai yi kokari don ganin kan al\’umma ya
hadu. Da aka tambaye shi akan ya ya zai yi? Sai ya ce ai kusan dukan
abin da ake nema don hadin kan kasa na nan kusa, to haka hanyoyin
hadin kan al\’ummar musulmai na nan wato kamar hanyoyi son juna da
kaunar juna duk Allah (SWT) Ya shimfida mana su kana su kuma
manya-manyan malamai shehunanmu na addini gaskiyar magana su hada
kansu tare da dinke barakar dake tsakaninsu ta yadda za a kauce fifita sashi ko
zargin juna wadda hakan kan taso lokaci zuwa lokaci domin daga na gaba kan
ga zurfin ruwa.
Ya kara da cewar akwai bukatar da su kansu rukunonin gwamnatocin kasar
nan uku wato gwamnatin tarayya da ta jihohi da na kananan hukumomi
musamman ma kuma gwamnatin tarayya nan gaba in har za su kira wani
taro don hadin kai ko makamancin hakan to akwai bukatar da bayan sun
kira shugabannin da akasari su ake kira a kullum zama a kuma nemo
dukkan bangarorin shugabannin addini da manya-manyan limamai don sa su
cikin zaman matukar an yi haka labudda duk wani sakon da ake so ya isa
ga al\’ummar musulmai don hadin kai zai isa.