GWAMNATIN YOBE TA KAFA KWAMITI NA MUTANE 8 DA ZAI ZAKULO TAKAMAMMEN TARIHIN BIRNIN NGAZ

0
1028
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
GWAMNATIN Jihar Yobe ta nada wani kwakkwaran kwamiti mai mutane 8 don
zakulo takamammen tarihin birnin nan na Ngazargamu da yake shi ne
hedikwatar tsohuwar Daular Kabilar Bare-bari ta kanem-Borno ta yadda
za a inganta shi don samar da abin tarihi ga al\’ummar Jihar Yobe da
yankin arewa maso gabas da ma kasa kasa baki daya.
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin Daraktan kula da harkokin yada
labarai da \’yan jaridu na gwamnan Jihar Alhaji Abdullah Bego a
tattaunawarsa da wakilinmu kan wannan lamari a garin Damaturu.
Ya kara da cewar,wannan tsohon birni mai dogon tarihi na Ngazargamu
gari ne da ya taba zama babbar hedikwatar tsohuwar Daular Kanem Borno
da ta yi yayi sama da shekaru dubu da suka shude, kuma garin na gab da
garin Geidam ne a Jihar Yobe kana ya yi iyaka da  kasar Jumhuriyar
Nijar.
Daraktan ya ci gaba da cewar wannan kwamiti mai mutane 8 da Gwamna
Alhaji Ibrahim ya amince da kafa shi na tuntunin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar Alhaji
Baba Malam Wali  sai mambobin kwamitin sun hada da Farfesa Yakubu
Mukhtar na jami\’ar Jihar Yobe a matsayin mai rufa masa baya.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Malam Hassan Gana babban sakatare
a ma\’aikatar kula da harkokin siyasa sai Dokta Ali Manzo Usman da Malam
Abubakar Garba na jami\’ar Maiduguri da Malam Lawan Abba Shettima da
kuma Muhammad Abare a matsayin sakatare.
Alhaji Abdullahi Bego ya ce babban aikin kwamitin shi ne kokarin tara
muhimman  abubuwa na tarihin wannan gari na Ngazargamu don saboda ya
zama abin tarihi ga al\’umma ta yadda kan iya jawo hankalin masu yawon
shakatawa na cikin gida da wajen kasa da ya ke gari ne da ke da dogon
tarihi da wannan yanki na arewa maso zai yi fahari da shi.
Ya kara da cewar wannan aiki da wannan kwamiti zai yi zai sake fito da
tarihi da hoton al\’ummar wannan yanki na mu musamman ganin cewar
wannan tsohuwar Daula ta Kanem Borno daula ce da ke cikin dadaddun
dauloli a Nahiyar Afirka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here