Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
TSOHON shugaban rusasshiyar jam\’iyyar PRP Halifan marigayi Malam Aminu
Kano kuma daya daga cikin \’yan kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin
kasar nan Galadiman Damaturu Alhaji Hassan Yusuf ya bukaci bangaren
shari\’a da alkalan kasar nan da su yi kokarin daidaita sahu a bangaren
na shari\’a don dawo da martabar sashin.
Tsohon mamban kwamitin gyare-gyaren tsarin mulkin ya bayyana hakan ne
ga GTK a garin Damaturu dangane da yadda alkalan suke yanke hukunci a
kotunan sauraren kararrakin zabe mabanbantan hukunce-hukunce bisa
kararrakin da aka rika kaiwa gabansu da sauran kararrakin da al\’ummomi
ke kaiwa.
Galadiman ya ci gaba da cewar, lokaci ya yi da bangaren shari\’ar kasar
nan zai dawo da martabarsa ta yadda masu shari\’a za su rika yin
tsayuwar daka don ganin suna yanke hukunci kamar yadda yake a kundin
tsarin mulkin shari\’ar kasa ba tare da kawo rudani ba.
Ya ci gaba da cewar, kamar yadda wasu alkalai suka rika yanke hukuncin
shari\’ar kararrakin zabe abin akwai rudarwa matuka don wasu alkalai
sukan ce amfani da na\’urar nan ta tantance masu kada kuri\’a wato (card
reader) ba ta cikin doka amma kuma wasu alkalan kuma suka ce ai amfani
da wannan na\’ura na da matukar muhimmanci ga dokokin hukumar zabe na
kasa da ke da nauyin shirya zabukan da ake kalubalantar nasarorinsu
gaban kotunan.To ai ka ga anan lamuran shari\’ar na da matukar sarkakkiyj
Alhaji Hassan Yusuf ya ci gaba da cewar, duk da cewar lamarin shari\’a
ya kunshi abu uku. Wato da farko akwai masu shari\’ar kansu na biyu
kuma akwai masu kara na uku kuma akwai mu \’yan kallo to amma su masu
suke da muhimmanci fiye da dukannin bangarorin biyu, don haka ya zama
wajibi bangaren na shari\’a da ya hada da alkalai da lauyoyi su yi abin
da ya dace don kauce wa ire-iren abubuwan da suka faru a baya musamman
dangane da sharu\’un zabe yadda a baya hukunce-hukuncen da alkalai suka
rika yi ke cin karo da junansu kamar yadda ya rika faruwa lokacin
zaben marigayi Abiola ta yadda wata kotun Legas za ta yanke hukunci
wata kotun kuma a Abuja ta yi nata hukuncin da ya sha banban da na waccar
kotun alhali a kan abu guda ne.
Dangane da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke a kan
zaben gwamnan Taraba da kotun ta ce ta ba da nasarar ga \’yar takarar
jam\’iyyar APC saboda shi gwamnan da ya fito daga jam\’iyyar PDP bai
shiga zaben share fage ba ai ka ga hakan ya yi daidai tun da yake ai
doka ta ce in baka shiga zaben share fage ba amma kuma ka tsaya takarar
babban zabe duk kuri\’un da aka jefa maka tamfar babu ne. To ai ka ga
wannan hukunci na kotu da ta yi ya yi daidai.
To amma da yake ita dokar kotu da dokar kasa kowa na mata fassarar da
ya ga dama ne akwai a karshe sai ga kotun koli ta ba da nasara ga Gwamna
mai ci na jam\’iyyai adawa ta PDP.
Don haka ne Galadiman na Damaturu sai ya shawarci alkalai da su rika
shirya tarukan bita don kara fahimtar juna a tsakaninsu tare da bitar
shari\’un baya don kokarin tsayar da gaskiya da adalci a shari\’u ganin
cewar a halin yanzu canji ya wanzu a kasa.