MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
KWAMISHINAN ’yan sandan Jihar Delta Zanna Ibrahim, ,ya sanar da kama
wasu jami’an‘yan sandan kwanu da ake yi da laifin kashe direban wata
mota mai suna Ejovwokereoghare, kusa da kauyen Emede, na jihar.
,Yan sandan uku suna aiki ai runduna ta 33 da ke Ado Ekiti , Jihar
Ekiti.Kwamishinan ‘yan sandan Ibrahim ya boye wa manema labarai sunayen
‘yan sandan moba da suka yi kisan kan amma ya ce “za a kai su kotu a kan
zargin sun yi kisan kai da kuma nuna rashn kwarewar aiki”.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Delta ya ci gaba da bayar da bayanin cewa
“’yan sandan suna aikin rakiyar wani daraktan kamfanin Jonesco mai
suna Arigbogha Johnny, kan titin filin jirgin sama da ke garin Warri
a lokacin ne suka yi kisan da ake zargin su da aikatawa”.
Ya kara da cewa wata mace da ke gefen hanya mai suna Agwere Hannahta ce
ta sanar wa da ofishin ‘yan sanda cewar “suna tare da wanda suka
kashen a gefen hanya, ‘yan sandan sun zo wucewa a wata mota kirar Hilux
mai lamba PF 297 SPY, lokacin su kuma sun dawo daga wurin biki kauyen
Emeden ,ita dai matar ta samu raunuka sakamakon harbi da aka yi musu
Yayin da shi kuma harsashi ya yi masa jina-jina aka kwashe su zuwa
babban asibitin Olomoro, nan ne likitoci suka tabbatar musu mutumin ya
mutu” inji shi.