MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
RUNDUNAR ‘yan sandan Jihar Ribas ta sanar da kubutar da daukacin
fasinjojin motar nan 14 da wasu ‘yan bindiga suka kama suka yi garkuwa
da su kwanan baya a mahadar babbar hanyar east- west da ke mararrabar
Ndele.
DSP Nnamdi Omoni kakakin rundunar ne ya sanar da haka ga GTK, inda
ya ce “bisa umarnin kwamishinan ‘yan sandan Ribas kwararru kan harkokin
ceto rayukan jama’a na rundunar ne aka baza su, kuma suka yi katarin ceto
su fasinjojin goma sha hudu.” Haka nan kuma rundunar ta gode wa kokari
da hadin kai na al’ummar da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da mutanen
suka bayar har aka cimma nasarar kubutar da su.
Dagan an jami’in ‘yan sandan ya kara da cewa ina mai tabatar muku duka
mutanen 14 an kubutar da su da rayukansu babu wani wanda ya mutu ko
ya yi kwarzane..Idan ba a mance ba ranar wata Litinin ce wasu mahara
suka yi wa motar fasinja kwanton bauna a mahadar Ndele suka kwace motar
da fasinjojin ciki zuwa wata maboya .