ALLAH NE YA SAKE DAWO DA BUHARI DON YA CI GABA DA CETO NIJERIYA-ARCHIBISHOP KAIGAMA

  0
  708

  Isah Ahmed, Jos 

  ARCHIBISHOP Ignatius Kaigama shi ne Archibishop na darikar katolika na Jos kuma shugaban bishop bishop na darikar katolika a Nijeriya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan masu kiraye kirayen a raba Nijeriya, ya bayyana cewa raba Nijeriya ba shi ne mafita ba. Ya ce al’ummar Nijeriya su rike gaskiya shi ne mafita. Har’ila yau ya bayyana cewa Allah ne ya sake dawo da shugaban kasa Muhammad Buhari domin ya ci gaba da ceto Nijeriya daga mawuyacin halin da ta shiga.

  Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

   

  GTK; Mane ne za ka ce kan masu kiraye kirayen a raba Nijeriya da masu kiraye kirayen a sake fasalin  Nijeriya?

  Archibishop Kaigama; Zancen a raba Nijeriya ba zance ne mai ma’ana ba. Domin Allah ne ya hada mu wuri daya a Nijeriya. Don haka zancen a raba Nijeriya bai taso ba. Idan bamu iya zama tare ba a Nijeriya, ko an raba Nijeriya 30 damuwar da muke da shi a Nijeriya zata cigaba a sababbin kasashen Nijeriya 30, idan aka raba. Don haka idan ana neman gyara ne a Nijeriya ayi aiki da gaskiya, idan muna aiki da gaskiya ba zamu sami damuwa ba. Idan ana amfani da kudaden da Allah ya bamu kamar yadda ya kamata, ba aji wani  mutum daya ya kwashe biliyoyin naira ba.  Duk abin da ake da shi za a yi amfani da shi ta yadda zai amfani kowa da kowa, ba za a sami matsala ba.

  Ba maganar raba kasa bane. Zancen ayi gaskiya ne a Nijeriya, zancen ayi kwazo  kowa ya tsaya yayi aikinsa  tsakani da Allah kan gaskiya ne ake bukata.  Idan aka raba Nijeriya za a gadar da matsalolin da muke fama da su zuwa ga sabbabin kasashen da za a raba.  Don haka gara mu cigaba da zama tare.

  Maganar sake fasalin kasar nan yana da kyau, domin idan dan’adam yana raye ya rika sake fasali daidai ne. Amma wanne irin fasali ne ake son a sake a Nijeriya? Ba  dai  maganar a raba kasar nan ba. A nemi hanyar da za ayi gyara ayi abubuwan da zasu amfani al’ummar Nijeriya da kara daukaka rayuwar al’ummar Nijeriya ne ake bukata. 

  Idan wasu suna ganin ana ci masu tuwo a kwarya ne, suna neman ayi gyara, wannan daidai ne. Amma wai maganar raba kasa ko kuma a tara dukiyar kasa a baiwa sashi daya, wannan bai taso ba. Allah ya bamu wannan arziki  ne tare. Akwai lokacin da a nan Jos ana hakar ma’adanin karafa, ana kaiwa kasashen waje ana samun kudaden shiga wadanda aka yi amfani da su a Nijeriya gabaki daya a lokacin.

   Yanzu akwai arzikin mai a kasar nan, ya kamata  wannan arzikin mai ya amfani kowa da kowa a Nijeriya. A raba komai daidai ta yadda kowa zai samu ya amfana. Wuraren da ake hakar mai a kula da su. A basu abin da zasu cigaba da shi, domin basu da kasar noma ko kamun kifi a wurarensu, don haka dole a lura da su.

  Kasarmu Nijeriya kasa ce mai albarka kuma Allah ya bamu albarkar yawan jama’a. Kwantar da hankali shi ne damuwa a Nijeriya. Yanzu a Nijeriya zaka ji a gabar akwai damuwa a kudanci da yammacin kasar nan haka suke. Maimakon mu tara hankulanmu mu hada kai muyi abubuwan da zasu taimakemu mun tsaya muna nuna banbancin kabila da addini. Maimakon wadanda Allah ya basu mukamai a kasar nan na shugabanci su nuna alheri su nuna gaskiya su bautawa jama’a sun kasa yin haka. Don haka muke fama da wahala a qasar nan.

  Allah ya bamu shugaban kasa mai kwazo da gaskiya ya kamata kowa ya rike gaskiya a Nijeriya tun da Allah ya bamu wannan shugaba. Domin shi shugaban kasa Buhari yana yin shugabancin  gaskiya a kasar nan. Don haka ina kira ga al’ummar Nijeriya mu kwantar da hankalinmu muyi aiki tare mu manta da maganar banbance. Idan muka yi haka zamu sami cigaba a Nijeriya, zamu sami nasara fiye da kasashen turawa.

   

  GTK;  Mane ne za ka ce dangane da dawowar shugaban kasa Muhammad Buhari daga jinyar da yaje waje da kuma abubuwan da kake ganin ya kamata ya mayar da hankali a kai?

   

  Archibishop Kaigama; Da dawowar shugaban Kasa komai ya canza a Nijeriya. A lokacin da yake waje kowa yana ta surutu. Amma daga isowarsa duk masu surutu kowa ya yi shiru komai ya lafa. Wannan ya nuna cewa shugaban kasa Buhari mutum ne mai daraja wanda mutanen Nijeriya suke kauna da girmamawa.

  Allah ya dawo da shi lafiya domin ya cigaba da bautar kasar nan. Akwai aikin da Allah ya bai wa shugaba Buhari a Nijeriya bai yi rabi ba. Yazo da niyyar gyara a Nijeriya amma akwai wadanda basa son wannan gyara da yake yi. Suna son a cigaba da zamba da cuta a Nijeriya.

  Don haka ina kira shugaba Buhari  ya kara sanya ido kan gyaran da ya zo yi a Nijeriya. Maganar yaki da cin hanci da rashawa ya rufe ido ya cigaba da wannan aiki. Ko waye ko dan jam’iyyarsa ne ko dan wata jam’iyya ne aka kama da laifi kan wannan al’amari na cin hanci da rashawa ya tabbatar  an hukumta shi. Ya samu ya tattara dukkan abubuwan da aka sace. Domin talakawa suna shan wahala a kasar nan. Muna da yara da dama wadanda basu da aikin yi a basu aiki yi. Wadanda suke tare da shi wato ministoci  da masu taimaka masa su zamanto masu gaskiya da rikon amana. Mun tabbatar idan shugaba Buhari ya cigaba da wannan gyara da ya sanya a gaba za a sami sauki a Nijeriya. Dubi irin amfanin gonar da Allah ya bamu a daminar bana duk inda ka duba a jihohin arewa ga amfanin gona nan ya yi kyau ga shinkafa da masara da dawa nan duk sun yi kyau. Gwamnati ta bude gonaki ta samarwa da al’umma taki da irin shuka da taraktocin noma  kan farashi mai rahusa.

  ,

  GTK; Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar kasar nan?

   

  Archibishop Kaigama; Sakona ga al’ummar Nijeriya shi ne muyi kokari mu zama daya, kada mu yarda wani ya rudemu mu rabu. Idan muka rabu zamu shiga wahala don haka muyi kokari mu zama daya. Domin a nan arewa muna da abin da mutanen kudu suke bukata, a kudu suna da abin da muke bukata a arewa. Mu hada kai muyi amfani da karfi da ilmi da dukiyar  da Allah ya bamu  idan muka yi haka zamu sami ci gaba a Nijeriya. Yadda Turawa za su yi fada kan neman izinin zuwa Nijeriya domin su zo su zauna.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here