KUNGIYAR MAGOYA BAYAN BUHARI ZA SU YI TARON GANGANMI NA MUTUM MILIYAN BIYU

0
653

Isah Ahmed, Jos

KUNGIYAR yakin neman zaben shugaban kasa Muhammad Buhari ta Buhari Campaign Organisation[BCO]  zata shirya gagarumin taron ganganmin nuna goyan baya ga shugaban kasa Muhammad Buhari na mutum miliyan 2 a ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, a babban birnin tarayya Abuja. Ko’odinaten kungiyar na kasa  kuma sakataren kungiyar dillalan mai ta kasa Alhaji Danladi Garba Pasali ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos.

Ya ce kungiyar tana nan tana tattaunawa da kungiyoyi guda 44 don shirya wannan  taron gangami na mutum miliyan 2 a ranar 1 ga watan oktoba, don nuna goyan baya ga gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari kan shirinsa na yaki da cin hanci da rashawa, da kuma nuna goyan baya kan yaki da maganganun batanci da ake yi a kafofin sadarwa na yanar gizo.

Ya ce babban abin da ya karfafawa kungiyar shirya wannan taron gangami na nuna goyan baya, shi ne ganin yadda duniya ta yarda cewa lallai shugaban kasa Buhari da gaske yake kan shirinsa na yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya.

‘’Shugabannin kasashen Afrika ta yamma gabaki daya  a wajen taronsu sun bayyana  cewa shugaban kasa Buhari  ne na daya wajen yakin da cin hanci da rashawa a Afrika ta yamma. Don haka suke  koyi da shi wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasashensu. Haka kuma kungiyar tarayyar turai ta cire Nijeriya daga cikin manyan kasashen da suke cin hanci da rashawa, sakamakon wannan yaki da cin hanci da rashawa da shugaba Buhari yake yi’’.

Alhaji Danladi Pasali ya yi bayanin cewa talakawan Nijeriya sun gane cewa shugaba Buhari yazo ne don ya ceto Nijeriya, don haka  suke cigaba da goyan bayansa.

Ya ce duk wani manomi a Nijeriya yaga irin kokarin da shugaban kasa ya yi wajen bunkasa aikin noma  a Nijeriya, ta hanyar  kare darajar amfanin gonar da manoma suka noma.

Ya yi kira ga al’ummar Nijeriya su fito su mara masu baya kan wannan taron gangami da zasu shirya, domin a karawa shugaban kasa kwarin gwiwa kan kokarin da yake yi, na ceto kasar nan daga mawuyacin halin da ta shiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here