MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
WANI jami’in ’yan sanda da ke aiki a rundunar ‘yan sandan Jihar Ebonyi
mai suna Donatus Oyibe,ya fada rijiya ya kashe kansa a wata mahadar
hanyar Ukwuakpu zuwa Abakaliki.Jihar Ebonyi.Dan sandan wanda asali
dan kauyen Oyibe ne yankin Ndiagu Ishieke, da ke karamar hukumar
Ebonyi.
Bayanai da wakilinmu na kudanci ya samo daga makusantan dan sandan
sun yi nuni da cewa Donatus Oyibe ya fada rijiya ce saboda an yi masa
sauyin wurin aiki daga jihar zuwa Borno shi kuma ya yanke shawarar mai
makon ya tafi bayan da takardar sauyin wurin aikin ta fito masa a
watan jiya sai ya tafi rijiya kamar zai debi ruwa daga nan sai kawai
ya yanke shawarar fadawa ciki mutane da suka zo wurin dibar ruwa suka
ga abu kamar almara ya fada cikin rijiyar inji majiyar.
Babbar ‘yar mamacin mai suna Ukamaka ta shaida wa manema labarai
cewar “babana ya dauki bokiti ya ce zai tafi rijiya dibar ruwa yana
zuwa tun da ya fita bai dawo ba har tsawon wani lokaci ba mu ga ya dawo
ba shi ne sai suka bi sawu zuwa rijiyar ko da suka isa wajen sun
tarar da bokitin da ya je da shi waje daya a bakin rijiyar amma shi ba su
gan shi ba shi ne da suka leka cikin rijiyar suka gan shi ya taso kan
ruwa ya riga ya mutu”inji ,yar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ebonyi Loveth Ogah
ta boye sirrin afkuwar lamarin amma ta ce nan gaba za ta yi magana da
zarar sun samu tabbacin hakan.