Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
GWAMNAN Jihar Yobe Alhaji Ibrahim ya amince da ware zunzurutun kudi har Naira Miliyan 323 don biyan Malaman makarantun Firamare kudadensu na ariyas ga wadanda aka ciyar da su gaba na karin matakin albashi daga watan Maris na wannan shekara ta 2017 zuwa watan Yuli.
A wata takardar sanarwa dake dauke da sa hannun Daraktan kula da harkokin yada labarai na gwamnan Alhaji Abdullahi Bego wacce aka raba wa manema labarai ciki har da wakilin GTK ta bayyana cewar wadannan kudade, kudade ne na ciyar da malaman gaba da aka yi da ya kama daga watan Maris zuwa watan Yuli na wannan shekara ta 2017 wadda tun a watan Augusta ne malaman da wannan karin ya shafa suka fara cin gajiyar wannan karin albashi na sabon matakin albashi da suka hau kai.
Bayanin ya ci gaba da cewa, gwamnan ya kuma amince da ware kudi kimanin Naira Miliyan 131,379,385,00 don biyan ma\’aikatun kananan hukumomi da yawansu ya kai kimanin 229 kudadensu na sallama (gratuity), cikinsu har da malaman makaranta da kuma wasu ma\’aikatan kiwon lafiya.
Gwamnan ya kuma bada tabbacin cewar gwamnatinsa za ta ci gaba da biyan dukannin hakkokin ma\’aikatan da suka dace.