Ambaliyar Ruwa: A\’isha Buhari Ta Tallafa Wa Jama\’ar Binuwai

0
712

Zubair A Sada, Daga Kaduna

UWARGIDAN shugaban kasa, Muhammadu Buhar, A\’isha Buhari ta nemi \’yan Najeriya masu kishin kasa da al\’ummarta da su tallafa wa jama\’ar Jihar Binuwai da ambaliyar ruwa ta auka masu, kuma suka rasa muhallansu na kwana a halin yanzu.

Tawagar uwargida A\’isha wadda uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa, Hajiya Mairo Almakura ita ce ta shugabanci tawagar uwargida A\’isha tare da SSA Dokta Hajo Sani sun isa Mkurdi babban birnin jihar suka zarce kai-tsaye zuwa babbarkasuwar nan ta zamani inda a nan fihe da mutane dubu biyar (5,000) suka sami matsugunni dalilin lalacewar muhallansu sakamakon ambaliyar ruwan.

Hajiya Mairo ta ce, uwargidan shugaban kasa ta ce babu shakka yawancin wadanda al\’amarin ya shafa mata ne da yara kanana, shi ne ta aiko da sakonta a karkashin shirin nan nata na tallafa wa mata da yara kanana da abinci kamar su shinkafa da gari da tumatiri, da abinci nau\’i-nau\’in wannan lokaci da kuma abinci na yara kanana da sauransu.

Da yake karbar kayayyakin a madadin gwamnatin jihar, mataimakin gwamnan jihar Injiniya Benson Abounu ya ce, yunkurin ceto rayukan al\’umma da uwargidan shugaban kasa Buhari take yi a shirin nan nata fitacce, abin a yaba ne kuma a kwaikwayeta. Sai ya ba da tabbacin cewa, za su raba kayayyakin yadda ya kamata ga al\’ummomin da al\’amarin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here