FADAR SHUGABAN KASA TA MUSANYA ZARGIN DA AKE WA GWAMNA GANDUJE

0
685
Daga Usman Nasidi

AN jawo hankalin fadar shugaban kasa ga rahotanni cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ki sauraron gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano a lokacin bikin murnar sallar Eid-el-Kabir da aka yi a kwanakin baya, wanda shugaban ya yi a garinsa Daura da ke Jihar Katsina.
Wannan rahotanni ta kasance daga masu neman ba ta siyasar gwamnan ne, wadanda suke so su yi amfani da al’amarin don cimma wani buri.
Mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina ya ce: ‘’Shugaban kasar ya karbi gwamna Ganduje tare da wasu gwamnoni makonni da suka wuce a Landan, kuma gwamnan ya yi maraba da shugaban kasar, tare da sauran mutane a lokacin da shugaban ya dawo kasar a ranar 19 ga Agusta.
Mene ne ya sa shugaba Buhari zai ki sauraron sa kamar yadda aka ruwaito, musamman a kan kafofin watsa labarai?\”
Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin bikin sallah a Daura
Gwamna Ganduje ya ziyarci Daura a lokacin bikin Sallah don ya yi ta’aziya ga sarkin Dauran, mai martaba Faruk Umar Faruk, wanda ya rasa wani ɗan\’uwansa, Barden Daura. Daga nan sai Gwamnan ya yi amfani da damar don ya kasance a bikin Eid-el-Kabir a garin.
KU KARANTA: Fallasa: An ji Mamman Daura da abokinsa na gulmar A\’isha Buhari a waya suna cewa,
\’\’ babu wani dalili da zai sa shugaba kasa ya ki sauraron Gwamna Ganduje, wannan ba ya cikin halin shugaba Muhammadu Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here