MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
HUKUMAR da ke ya yi da shan miyagun kwayoyi da kuma hana fataucin su NDLEA da ke Jihar
Kuros Riba ta kama wasu mutum biyu da suka goge wajen sarrafa miyagun kwayoyi da kuma
ganyen tabar wi-wi matsayin abincin gwangwani ko kayan makulashe suna sayarwa wanda a
zahiri za a ga hakan amma idan an bude babu komai ciki sai kayan maye tsabarsa mutanen biyu
Christian Chindu Joseph, dan shekara 37 da haihuwa da kuma Edet Bassey Edim,dan shekara
30 da haihuwa an kamasu a inda suke sarrafa kayan mayen dake layin Akim Close, Unguwar
Akim kana kuma da layin Akim road, dukkan su a Kalaba sun shiga hannu ne bayan da aka
kyankyasa wa jami\’an irin abin da suke yi.
Jami\’in hulda da jama\’a na hukumar NDLEA Odili Kenneth, ya sanar da haka ga wakilinmu na
kudanci yace wadanda ake zargin suna hannun su ana tsare dasu yaci gaba da cewa daya daga
cikin wadanda ake zargin da yana aiki a wani gidan sayar da kayan lashe-lashe da tande-tande a
Fatakwal ya bari ya dawo kalaba yaci gaba da yin irin harkar amma shi yana sanya kayn maye a
ciki yayin das hi kuma Edet Bassey yake kawo basa ganyen tabar wi-wi din yana sarrafawa.
Mai magana da yawun hukumar ya ci gaba da cewa har wayau hukumar su sun kama Diyaolu
Oluwaseun Dare, dan shekara 27 da haihuwa da ya yi safarar hodar iblis kuma ya zo tashar
jiragen ruwa ta Kalaba zai karbi kayan aaka kamashi wanda har ma abokin huldarsa mai suna
David Okla James, dan shekara 35 da haihuwa aka bi shi har garin Ugep.,shi ma aka kama shi .
Karin wasu mutanen da hukumar NDLEA a Kuros Riba ta ce ta kama da wani gurgu ma a kauyen
Iwuru da aka sameshi da tarin gayen tabar wi-wi sauran wadanda suka hannu inji shi sun hada da
“James da aka kama shi da hodar iblis mai nauyin kilo 1,764, a mararrabar Army junction da ke
kalaba
Haka nan kuma an kama Gabriel Effangh da Offiong Ekeng da ke kauyen Eto Mkpe, sannan
Effiong Joseph, da aka samu da hodar iblis shi ma mai nauyin kilo a 76 1.83. Ana zargin laifin da
suka aikata ya saba dokar kasa inji mai magana da yawun NDLEA