\’YAN FASHI SUN KASHE MUTANE 2 DA JARIRI A JIHAR KADUNA

0
687
Daga Usman Nasidi
KIMANIN mutane hudu ne suka rasa rayukansu sanadiyyar wani hari da yan fashi suka kai musu a kan hanyarsu ta zuwa jihar Kwara, a babbar hanyar Birnin Gwari.
Bincike ya nuna cewa wani daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya, wanda jami’in hukumar kwastan ne ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Lahadi 10 ga watan Satumba.
Majiyarmu ta ruwaito \’yan fashin da adadin su ya kai mutane 20 sun bude wuta a jerin gwanon motocin kamfanin Kwara Express su uku da ke dauke da fasinjoji ne a daidai kauyen Palwaya.
Mutumin ya ce \’yan fashin sun yi ma direban motar nuni  da ya ci birki, ya tsaya a gefen hanya, amma sai direban ya yi yunkurin tserewa, daga nan ne fa suka bude ma motar wuta, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar hafsan soja, David Ejisoro mai mukamin Kyaftin,tare da wani jariri.
Hakazalika, akwai wasu mutane gud 2 da ke cikin motar da suka mutu sakamakon harbin, sai kuma uwar jaririn, wanda ita ma aka harbe ta a kan mama.
Bayan harbin ya tsagaita, an garzaya da mutanen zuwa babban asibitin Birnin Gwari, inda aka binne jaririn, bayan da mahaifiyarsa ta sanar da mijinta.
Jim kadan da faruwar lamarin, sai jami’an tsaro da dama suka dira inda lamarin ya auku, sa’annan suka bude hanyar, bayan an rufe ta na tsawon awanni, daga bisani kuma suka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa cikin garin Kaduna don samun kulawa mai kyau a kwararrun asibitoci.
Kakakin \’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mukhtar Husseini Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya tabbatar da mutuwar mutane 3.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here