AN NEMI GWAMNATIN TARAYYA DA KUNGIYOYIN BADA TALLAFI NA KASA DA KASA DA SU CIKA ALKAWURANSU GA AL\’UMMOMIN AREWA MASO GABAS

0
636
Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
SHUGABAN kungiyar hadakar \’yan kasuwa na karamar hukumar Potiskum  a
Jihar Yobe Alhaji Isa sakatare ya kirayi gwamnatin tarayya da kuma
daidaikun kungiyoyin bada tallafi na cikin gida da na waje da su
hanzarta wajen cika alkawuran da suka dauka na bada tallafin tun kafin
al\’umma su dawo daga rakiyarsu.
Shugaban ya bayyan hakan ne ga wakilinmu a ofishinsa da ke garin
Potiskum dangane da yadda aka sa mambobinsu ke ta cika takardu da
niyyar za a ba su tallafi da kuma rance amma har yanzu shiru kamar an
shuka dusa,
Alhaji Isa sakatare ya ci gaba da cewar, daga shekarar  2015 zuwa
wannan shekara ta 2017 an sa sun cika fom na neman rance da kuma neman
tallafi sama da 7 daga bankunan bada rance mai sauki ga
\’yan kasuwa da kuma kungiyoyin bada tallafi kan abin da ya shafi
yankunan da suka yi fama da rikicin Boko Haram na cikin gida da na
waje amma har yau babu koda guda da aka ba su.
Don haka ne suke kira ga dukan wadanda abin ya shafa da cewar, in har
da gaske ake yi kan kudirin taimaka wa al\’ummomin wannan yanki namu na
arewa maso gabas musamman Jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe da su
suka fi fuskanta radadin wannan rikici to akwai bukatar da fara
aiwatar da wannan kudiri, domin sun fara kosawa.
Daga nan sai shugaban kungiyar \’yan kasuwar ya nemi jama\’a da su
ci gaba da bada goyon baya ga wannan gwamnati ta shugaban kasa
Muhammadu Buhari dangane da muhimman kudirorinsa na ciyar da kasa
gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here