Babu Zancen Zaman Lafiya Cikakke Muddin Matasa Ba Su Da Aikin Yi -Inji Mamu

    0
    814
    Muhammad Sani Chinade, DAGA DAMATURU
    GTK ta samu tattaunawa da wani matashi Injiniya Mamu da ke rike da
    sarautar Tafarkin Dan Majen Katagum  da ke da kudirin samar da
    aikin yi ga matasa don kawar da zaman banza da yake cewar in ba an
    samar da aikin yi ga matasan ba to fa zancen zaman lafiya ga al\’umma
    babu shi, inda suka tattauna da wakilinmu Muhammad Sani Chinade. Ga yadda
    tattaunawar tasu ta kasance:-
    GTK : Ko mene ne ya ja hankalinka ka yi tunanin samar da aikin yi ga matasa?
    MAMU : Alhamdulillah dukan godiya da yabo sun tabbata ga Allah SWT. To a
    gaskiya ni yadda na dauki rayuwata ta’allaka ne a kan abu biyu ne na
    farko shi ne bautawa Allah SWT wanda ya halicce mu domin mu bauta
    masa abu na biyu kuma shi ne bauta wa mutane ta hanyar bada gudummawata wato abin
    da ake ce wa \’Service to humanity\’, ina ga duk inda aka zaga  aka zaga a
    rayuwa ake yiwa.
    Kuma kokarin samar wa da matasa aikin yi a gaskiya wadansu dalilai ne
    na kai na abin da ya shafi iyalaina shi ne da na ga kwalliya na biyan kudin sabulu sai kuma na
    fadada shi ya zuwa kan matasa wadanda sune kashin bayan kowace al’umma.
    Don haka dubawa na yi na ga cewar, babu amfani a matsayina na
    magidanci mai mata uku duk abin da ya taso ga matana sai sun zo waje
    na karbar kudade domin biyan wasu bukatunsu na yau da kuillum sai na
    ga hakan bai yi ba, maimakon hakan sai na yi nazarin saya musu Babura masu
     tayoyi uku-uku wato KEKE NAPEP ga kowaccensu don su samu hanyoyin
    shigar kudi ko na samu sauki wajen abin yau da kullum, to Allah cikin
    ikonSa wannan dabara da na yi sai ta haifar da da mai ido yadda ba ma ga su matana
    ba hatta su ma matasan da aka basu baburan don yin aiki da su su din ma rayuwarsu ta kayutatu.
    To wannan ne ya karfafa min gwiwar da na fadada wannan lamari har ga matasa yadda na sayi
    Babura masu tayoyi uku keke napep guda 25 hade da motoci da nufin inganta rayuwar matasan yadda na ba su haya cikin farashi mai sauki Naira dubu biyar a sati.
    GTK: Shin ko hakan da ka yi kwalliya ta biya kudin sabulu?
    MAMU: Kwarai da gaske kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu har ma da
    fankeke da gazal domin kuwa a halin da ake ciki wadannan matasan da na
    samar musu baburan su da iyalansu da abokansu da makanike da
    ire-irensu duka sun samu abin yi, kuma hakan ya sa rayuwarsu ta inganta fiye da yadda ta ke a
    baya ta yadda zaman banza da zaman daba ya kau daga gare su
    kasancewar rufin asiri daga Allah SWT Ya bayyana  a gare su.
    Ina wannan abu ne da zimmar kawar da zaman banza da matasan ke yi amma ba domin
    ya ci wata riba ba illa ribar da yake nema ita ce ya ga matasan sun
    samu abin yi sun daina zaman daba da shaye-shayen muggan kayayyakin sa
    mayen da ke iya haifar da aikata ta’addanci tsakananin al’umma.
    GTK: A matsayinka na ma’aikacin gwamnati kuma mai rike da sarautar
    gargajiya ko kana ga in da a ce al’ummarka za su neme ka da ka fito
    domin shiga siyasa don neman wani matsayi ko za ka amsa kiran su ta
    wajen barin aikinka don shiga harkokin siyasa?
    MAMU: To kamar yadda na fada ne a baya cewar na ta’allaka rayuwata
    ne kan abu biyu wato da farko na bauta wa Allah SWT,  na biyu kuma
    bauta wa al’ummata ta hanyar bada gudummawa ta wajen ci
    gabansu , to lalle in har al’umma ta sun neme ni da in fito domin
    shiga harkokin siyasa don neman wani matsayi, to ai ba ni da wani zabi illa in amsa kiransu domin komai daga Allah yake a kullum kuma addu’a ta shi ne Allah SWT Ya zabar min abin da ya fi
    alheri a rayuwata. Kuma ka sani cewar, a gaskiya ba ni da wani kudirin
    shiga harkokin siyasa to amma in Allah Ya sa hakan ne mafita to alhamdulillahi.
    GTK: Mene ne fatan ka kan al’amuran da suke addabar kasar nan ko
    kuma in ce yankin arewa maso gabas?
    MAMU: Fata ta ita ce, Allah SWT Ya taimaki wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammadu Buhari
    don ganin ta samu nasarar kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye
    wannan yanki namu dangane da matsalar Boko Haram duk da cewar ko yanzu
    ma Alhamdulillah. Da kuma sauran matsalolin da ke addabar kasa baki wadda su din ma akwai haske a kai

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here