GWAMNATIN FILATO TA KASHE NAIRA BILIYAN 4 WAJEN KUDADEN ‘YAN FANSHO

0
664

 Isah Ahmed, Jos

SHUGABAN riko na hukumar ‘yan fansho ta jihar Filato Barista Dashe Selfa Donpar ya bayyana cewa daga lokacin da gwamnatin jihar karkashin Gwamnan jihar Simon Lalong ta zo zuwa yanzu, ta kashe kudade  Naira Biliyan 4 wajen biyan kudaden fansho ga ma’aikatan jihar da suka yi ritaya. Barista Dashe Selfa Donpar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce tun farkon zuwan wannan  gwamnati ta Gwamna Simon Lalong sakamakon kudaden da shugaban kasa Muhammad Buhari ya bai wa jihar, ta sami nasarar biyan kudaden fansho na watannin 8 da ‘yan fanshon jihar nan suke bi bashi.

Har ila yau ya ce a lokacin da gwamnatin  ta zo ‘yan fansho a Jihar Filato mutum dubu 6 ne. Amma yanzu akwai ‘yan fansho kusan dubu 8 a Jihar Filato wadanda ake biyansu kudaden fansho a kowanne 25 na kowanne wata.

‘’Ko a wannan wata da muke ciki mun sanya sunayen ma’aikatan da suka yi ritaya  mutum 400  a jerin ‘yan fansho. Kuma za su sami kudadensu na fansho a wannan wata’’.

Daga nan ya yi kira ga ‘yan fansho na Jihar Filato su kara hakuri domin gwamnatin tana nan tana kokarin ganin ta biya su dukkan kudaden fansho da suke bi bashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here