MANOMAN FILATO SUN NOMA SHINKAFA EKA DUBU GOMA KARKASHIN SHIRIN FADAMA III

0
769

 Isah Ahmed, Jos

SHUGABAN shirin Fadama III a Jihar Filato Mista Gideon  Dandam ya bayyana cewa manoman jihar Filato karkashin shirin Fadama III mutum dubu goma ne suka noma shinkafa eka dubu goma a daminar bana. Mista Gideon Dandam ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce a wannan  shiri na Famada III a  Jihar ta Filato, tun da farkon damina an tallafa wa manoman ta hanyar  yi wa kowanne manomi  kaftu a gonarsa da ba shi irin shinkafa ingantatce da maganin kashe ciyawa da takin zamani buhu hudu na NPK da buhu biyu na Uriya a kan kowace eka daya tare da koya wa manomin yadda ake noma shinkafar. 

Ya ce  kananan hukumomin Jihar ta Filato  da aka yi wannan noman shinkafa sun hada da Mangu da Pankshin da Kanke da Wase da Langtang ta kudu da Langtang ta arewa da Kanam da Shendam da Qann Pan da Mikang da Bassa da Jos ta gabas da Barikin Ladi.

‘’Ya zuwa yanzu shinkafar da manoman suka noma ta yi kyau sosai da sosai, don haka manoman suna ta murna ganin irin dibbin shinkafar da za su samu. Kuma tuni sun kulla yarjejeniya da wani kamfani mai suna Tim Tali Rice Mill da zai sayi shinkafar  ya sarrafa ta’’.

Shugaban shirin na Fadama ya yi bayanin cewa babu shakka wannan Shinkafa da manoman Jihar ta Filato suka noma, idan ta zo ta fi karfin al’ummar Jihar Filato dole sai dai a fitar da ita zuwa wasu jihohin kasar nan.

Ya yi kira  ga gwamnatin Jihar Filato da sauran masu hanu da shuni su  kafa manyan injinan sarrafa shinkafa a  jihar, domin shinkafar da manoman suka noma  tafi karfin kamfani daya ya iya sarrafata.

Daga nan ya yaba wa  shugaban kasa Muhammad Buhari da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong kan kokarin da suka yi wajen  tallafa wa harkokin noma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here