MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga kalaba
SANA\’AR haya da doki a Kurmi wani sabon abu ne ga \’ya\’yan Hausawa da
aka haifa a can sannan kuma wani lamari ne na karin ilimi gare su
musamman wasu daga cikin haihuwar Kurmi ba su taba ganin doki a
zahirinsa ba sai dai ko a hoto ko kuma a fim. Da yawa ma cikin
halittun gida da suka hada da rakumi ,jaki da kuma kura, da biri a
halittun daji da ake shigowa gari da su gari ana yin wasa da su ana
samun abin sanyawa baki, ba kasafai yaran ke katari su gani ba.
A Jihar Kuros Riba musamman Kalaba babban birnin jihar da yake maraya
ce Isyaka Abdullahi wani dan asalin Jamhuriyar Nijar mazaunin Uyo,
jihar Akwa Ibom ya kawo doki Kalaba yadda \’yan asalin jihar da ma na
arewa suke biyan kudi kalilan suna hawan doki suna daukar hoto lamarin
da ya zame musu tamkar wani wanda ya je wata kasa yawon bude ido haka
kuma \’yan arewa da ba su taba ganin doki ba a zahiri sai a hoto na
tururuwa suna zuwa kallon doki suna biyan kudi ana dora su a kai suna
daukar hoto.
Wakilinmu na kudanci ya zanta da Isyka kan wannan sana\’a ko mai ya
ba shi sha\’awa har ya kawo doki Kalaba wasu ke biyan kudi suna hawa ana
daukar su hoto “ abin a yaba ne kuma a yi alfahari da shi domin ni kaina
idan na shiga wani wuri mutane kan gaya min cewa su ba su taba ganin
doki ba a fili sai a fim ko hoto amma yanzu ga ni sun gani suna
mamaki,dangane da dokin da na shigo da shi Kalaba, wasu har kudi suna
ba ni su hau su yi hoto, wani lokaci suna ba ni Naira 300 zuwa Naira 500
su hau “.Ya ci gaba da cewa kawo doki Kurmi ba karamin wayar wa da
mazauna yankin da ba su taba ganinsa ba kai ya yi musamman \’ya\’yan \’yan
arewa da aka haifa a Kurmi.
A kudancin Nijeriya masu sana\’ar yawo da kura zuwa biri na kara
wayar wa \’ya\’yan arewa da aka haifa kai domin wasu sai a fim ko hotuna
suke ganin irin wadannan dabbobi musamman mazauna jihohin kudu da
babu gidajen ajiye namun daji.Isyaka ya ce a rana ta Allah matukar ba
ruwan sama aka yi ba ya hana masa fita ba akalla “ina samun alheri
daga Naira dubu 150 zuwa fiye da haka a wata, a ciki ne nake ci nake
sha kuma nake kula da lafiyar dokin”inji shi.
A karshe ya ce abin da ya sa \’yan kudu ma za su iya kiwon doki ba ko wata
dabba babba saboda wajen ciyar da su da shayarwa kana da kula da
lafiyar dabba shi ke sanyawa su galabaita har su kai ga mutuwa “ za ka
ga an bar saniya ko akuya ta yini daure kafin a ba ta abinci ko ruwa ta
sha har sai ta fita hayyacinta, ka ga kamar doki ba ya son sanyi lokacin
damina a nan Kurmi sanyi yana yi wa doki illa har ya kai ga sawa yana
mutuwa idan ba a samu wanda zai kula da shi ba sosai”.Wakilinmu ya
zanta da wasu yara da suka hau doki game da basirar su akasarin su sun
bayyana cewa ba su taba ganin doki ba sai wannan karo sun saba gani a
fina-finai ko kuma a hoto.