IPOB: \’Yan Tawayen Biyafara Sun Kai Hari A Asaba

0
844
MUSA MUHAMMAD KUTAMADaga kalaba
AKALLA mutum biyar suka rasa rayukan su a  wani hari da ake zato \’yan
kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biyafara ne suka kai shi daren
Juma\’ar da ta gabata a kasuwar Abraka da ke Asaba babban birnin jihar
Delta.
Cikin wadanda suka gamu da ajalin nasu kamar yadda wata majiya
ta shaida wa wakilinmu a  garin Asaba fadar gwamnatin jihar, ta ce
biyu \’yan asalin jihar Nasarawa mace da kuma yaro karami  yayin da
sauran ukun  kuma ba,a tantance jihohin su na  asali ba
Maharan an ce da misalin karfe  goma sha daya na dare suka kutsa kai
zuwa unguwar suka fara harbe-harbe suka nufi masallaci da ke Layin
Cable Asaba a zaman daya daga cikin gari da ake ganin idan anjeshi
tudun mun-tsira ne wannan shi ne karo na farko da \’yan kungiyar IPOB
suka kai hari na huce takaici sakamakon gumurzu da suke yi da jami\’n
tsaro da kuma ,yan kungiyar masu fafutukar  a ware.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here