BAI KAMATA INYAMURAI SU GOYI BAYAN A RABA NIJERIYA BA-YAHAYA KEGA                    

0
695

 

Isah  Ahmed, Jos

SHUGABAN kungiyar dillalan sayar da motoci ta kasa reshen Jihar Filato kuma shugaban kamfanin sayar da motoci na Kega Motors da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega, ya bayyana cewa bai kamata al’ummar Inyamurai su goyi bayan a raba Nijeriya ba. Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu kan rikicin da ya faru a makon jiya,  inda masu fafutukar neman kasar Biyafara suka  kai wa ‘yan arewa mazauna  yankin Inyamurai hare-hare, wanda ya yi sanadin fara daukar fansa a garin Jos.

Ya ce wannan rikici wani abu ne marar dadin ji kuma  wani abu ne da aka yi na rashin kan gado. Domin ainihin wadanda suke tayar da wannan rikici, ba mutanen da suke zaune a Nijeriya ba ne, musamman shugaban kungiyar fafutukar yakin neman kasar ta Biyafara, Nnamdi Kanu.

Ya ce ya  kamata Inyamurai su fahimci cewa  ‘yan arewa sun karbe su hannu bibbiyu shekara da shekaru sun ba su masauki sun ba su komai na karramawa. Ya ce  idan aka ci gaba da wannan rikici Inyamuran ne za su cutu kuma su ne za su yi asara. Arewa babu wata asara da za ta yi, domin tana da kasar noma, tana da komai da komai na rayuwa.

Alhaji Yahaya Kega ya yi bayanin cewa idan aka kasa yawan arzikin arewa gida uku, kashi daya na Inyamurai ne. Kuma duk wani harkokin kasuwanci da za a yi a Nijeriya, dole sai an hada da Inyamurai. Don haka  idan da tunani mai dukiya ba zai so a yi fada ba.

Ya ce Illolin da wannan rikici zai kawo wa Inyamurai suna da yawa. Na farko za su yi asarar abubuwan da suka mallaka, kuma nan gaba babu wanda zai saki jiki ya sake hulda da su.

Ya yi kira ga al’ummar Inyamurai da sauran al’ummar Nijeriya su yi hakuri da juna su zauna lafiya domin a ci gaba da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here