Isah Ahmed, Jos
IMAM Ibrahim Awwal [Usama] shi ne Limamin masallacin gidajen ‘yan majalisar tarayya da ke zone B, Apo babban birnin tarayya Abuja. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa duk gwamnatin da ka ga ana yi mata zagon kasa a Nijeriya, ta mutumin arewa ce. Kuma munafukan ciki, mutanen arewa ne suke fara ba da kofa a ci mutumcin duk wata gwamnati ta dan arewa a Nijeriya. Don haka ya yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari ya cire mutanen da suka yake shi a cikin gwamnatinsa, domin har yanzu suna yi wa gwamnatinsa zagon kasa. Har ila yau ya yi tsokaci kan hare-haren da aka kai wa ‘yan arewa a yankin Inyamurai a makon da ya gabata, kan maganar neman kasar Biyafara da kuma yanayin tafiyar da mulkin dimokuradiyya a Nijeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
GTK; Mane ne ka fahimta dangane da yadda wasu na kusa da shugaba Buhari suka fara fitowa suna cewa ba za su mara masa baya ba, idan har zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben shekara ta 2019?
Imam Usama: Duk gwamnatin da ka ga ana yi mata zagon kasa a Nijeriya, ta mutumin arewa ce. Kuma munafukan cikin mutanen arewa ne suke fara ba da kofa a ci mutuncin duk wata gwamnati ta dan arewa a Nijeriya. Yau a Nijeriya akwai ministocin da suka fito suna fadin maganganun da suka ga dama. Dama tun daga fara kiran sunayen wadannan ministoci, mutane suka fara cewa za a sami matsala saboda mafiya yawansu masu laifi ne, domin sun aikata barna a baya. Wadannan ministoci da shugaba Buhari ya dauko ya ba su amana a cikin wannan gwamnatinsa sun ci amanarsa. Ya kamata su sauka daga kan mukamansu maimakon su rika cewa idan zai sake tsayawa ba za su goyi bayansa ba.
‘Yan adawa sun wahala a kasar nan a zamanin gwamnatin da ta gabata, amma da wannan gwamnati ta Buhari ta sami nasarar kafa gwamnati, sai ta dauko wadanda suka azabtar da ‘yan adawa a zamanin gwamnatinsu ta ba su mukamai. Akwai jami’an gwamnatin da ta gabata wadanda suka yaki wannan gwamnati a lokacin yakin neman zabe, amma abin mamaki har yanzu irin wadannan jami’ai suna nan kan kujerunsu suna yi wa wannan gwamnati zagon kasa.
Amma ‘yan adawar da suka taimaka wa wannan gwamnati ta Buhari wajen ganin kafuwarta an yi watsi da su, suna nan ana yi masu dariya.
Bai kamata wannan gwamnati ta ci gaba da barin irin wadannan mutane wadanda suka azabtar da ‘yan adawa su ci gaba da zama a cikin gwamnatin ba, domin za su ci gaba da yi mata zagon kasa. Domin ba sa tare da ita.
GTK: Mane ne za ka ce kan rikicin da yake faruwa na hare-haren da aka kai wa ‘yan arewa a yankin Inyamurai a makon da ya gabata, kan maganar neman kasar Biyafara?
Imam Usama: Wannan rikici da yake faruwa wani babban abin takaici ne. Jagoran kungiyar neman kasar Biyafara Nnamdi Kanu ya yi laifi ne aka kama shi, aka gurfanar da shi a gaban kotu. A lokacin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha an sami Ken Saro da laifi aka yanke masa hukumci kisa. Bayan haka a cikin kasar nan an zargi Obasanjo da yunkurin juyin mulki an yanke mana hukunci. An yanke wa marigayi Shehu Musa Yar’aduwa hukunci har ya rasa ransa a gidan yari. An kama marigayi Abiola ya rasa ransa a gidan yari. Shi kansa shugaban kasa na yanzu Muhammad Buhari ya zauna a gidan yari. Wane ne Nnandi Kanu da zai tayar da hankalin Nijeriya a zura masa ido. Kotu ta bayar da belinsa kan wasu sharudda ya saba wadannan sharudda, amma a ce ba a yarda a sake kama shi ba. Wannan yaro fa ba a Nijeriya aka haife shi ba, don haka yana da bizar zama a wasu kasashe. Bai kamata a sanya masa ido ba, wai don ana son a zauna lafiya.
Mutanen da ake tsare da su kamar Malam Ibrahim Zakzaky da Kanar Sambo Dasuki su ba ‘yan kasa ba ne da ake tsare da su? Su ma ‘yan Nijeriya ne kuma su ma suna da magoya baya, amma dole ne su bi dokar kasa. Don haka abubuwan da suke faruwa a yankin Inyamurai na cin mutuncin ‘yan arewa da suke zaune a can ba daidai ba ne.
Amma muna kira ga ‘yan Nijeriya musamman ‘yan arewa wannan mutum yana son a yi tashin hankali ne a Nijeriya. Don haka muna kira ga ‘yan arewa su yi hakuri kada su tayar da hankali dangane da abubuwan da suke faruwa.
GTK: To yaya kake ganin yanayin yadda mulkin dimokuradiyya yake tafiya a Nijeriya?
Imam Usama: Kuskuren da aka samu a Nijeriya kan mulkin dimokuradiyya shi ne har yanzu, zan iya cewa ba a fara mulkin dimokuradiyya ba a Nijeriya. Domin idan mutum ya tsaya ya lura a lokacin da muka fita daga mulkin soja a Nijeriya, bayan da aka yi ta kiraye-kirayen a koma mulkin dimokuradiyya, domin a sami walwala da ci gaba.
A lokacin sai aka ce duk kasar nan babu wanda zai fito takarar shugaban kasa sai Obasanjo da Olu Falaye. Wadannan mutane ba su kadai ba ne a Nijeriya, kuma ba su kadai ba ne za su iya wannan takara ba. Amma haka aka zuba ido aka fara kafa wannan dimokuradiyya da son zuciya. Saboda wai don a dinke barakar da ta taso sakamakon soke zaben Abiola na June 12.
Wannan shi ne ya fara jefa mulkin dimokuradiyya a cikin wani mawuyacin hali a Nijeriya. Domin da dimokuradiyya aka kafa ta gaskiya, wadanda suka fi yawa su ne duk abin da suka zaba za a bi.
Don haka aka ci gaba da samun matsala saboda ba a kafa mulkin dimokuradiyyar kan gaskiya ba.
GTK: Wato a ganinka sakamakon wannan matsala da aka samu, ba a sami ribar mulkin dimokuradiyya ba a Nijeriya?
Imam Usama: Gaskiyar magana amfanin mulkin dimokuradiyya da aka samu a Nijeriya ba shi da yawa. Domin satar kudaden da ake yi a lokacin mulkin dimokuradiyya a Nijeriya, ya fi sace-sacen kudaden Nijeriya da aka yi a lokacin da sojoji suke kan mulki. A lokacin mulkin dimokuradiyya za ka ga mutum daya ya debi biliyoyin naira ya tafi abinsa. Kuma ba a taba samun lokacin da ake daukar rayukan al’ummar Nijeriya, kamar a wannan lokaci na mulkin dimokuradiyya ba.
Sannan idan mutum ya lura babu lokacin da za ka je asibitocin gwamnati ka ga babu gadon kwanciya, babu magani kamar wannan lokaci na mulkin dimokuradiyya. Babu lokacin da hanyoyin kasar nan suka lalace kamar wannan lokaci na mulkin dimokuradiyya. Idan mutum ya dubi lokacin mulkin soja hanyoyin kasar nan ba su lalace kamar haka ba. Misali aikin gyara hanyoyin kasar nan da hukumar tara rarar kudin man fetur [PTF] ta yi lokacin mulkin soja na marigayi Janar Sani Abacha ya fi aikin gyaran hanyoyin da aka yi a cikin shekaru 8 na mulkin dimokuradiyya.
GTK: Wadanne shawarwari za ka bai wa shugaban kasa kan abubuwan da ya kamata ya yi don ganin an ceto al’ummar kasar nan daga mawuyacin halin matsin da suke ciki?
Imam Usama: Lallai al’ummar kasar nan suna cikin kuncin rayuwa kuma babu shakka har yanzu talakawan Nijeriya babu abin da suka gani a kasa. Lallai shugaban kasa Buhari ya sani cewa mafi yawaicin azaluman kasar nan har yanzu ba sa tare da shi. Amma Allah ya ga dama ya ba shi mulkin kasar nan. Kuma har yanzu wadannan azalumai ba sa tare da shi, suna nan suna ci gaba da yi masa zagon kasa. Sun yi duk kokarin da ya kamata su yi don su raba shi da talakawan Nijeriya. Amma saboda talakawan Nijeriya suna tare da shi ba su sami nasara ba. Don haka ya kamata ya waiwayi talakawan Nijeriya ya yi masu abubuwan da ya kamata domin ceto su daga cikin mawuyacin halin da suke ciki.