Daga Usman Nasidi
BABBAR kotun tarayya da ke a Abuja a Larabar makon jiya ta tabbatar tare da yanke hukunci cewar tabbas lallai kungiyar nan ta \’yan aware ta Indigenous People of Biafra (IPOB) a takaice da ke fafutukar ganin an kafa kasar Biyafa ta ta\’addanci ce kuma haramtacciya.
Haka ma dai kuma kotun ta tabbatar da haramtar kungiyar tare kuma da shafawa dukkan mambobin ta bakin fenti a ko ina suke a fadin duniya baki daya.
Majiyarmu ta samu labarin cewa a hannu guda kuma tuni dai wasu mambobin suka yi fatali da hukuncin kotun inda suka ce shugaba Buhari ne kawai ya juya akalar Alkalin shi kuma ya yanke hukunci.
A wani labarin kuma Gwamnonin arewacin Najeriya sun bayyana cewa matsalolin da bangaren kudu maso gabashin kasar kwata-kwata basu da alaka da kuskuren fahimtar da ake yi na cewa wai ba a damawa da \’yan yankin a harkokin gwamnati.
Gwamnonin sun bayyana cewa akasin hakan ma dai shi ne yadda hasali yan kabilar ta Ibo suka rike manya-manyan mukaman kasar nan kamar na Sakataren gwamnatin tarayya da kuma shugaban majalisar dattijan kasar da ma sauran su