MA\’AIKATAN LAFIYA SUN TAFI YAJIN AIKIN DA BABU RANAR DAWOWA

0
607
Daga Usman Nasidi
KUNGIYAR ma’aikatan lafiya a ranar Larabar makon jiya ta bayyana tafiya yajin aiki ta kasa da babu ranar dawowa.
Shugaban kungiyar JOHESU na kasa, Mista Biobelemoye Josiah ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a Ilorin, babban birnin jihar Kwara a ranar Laraba inda ya ce za a soma yajin aikin a ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa a ranar 14 ga watan Agusta kungiyar ta ba da wa’adi na adadin kwanaki 30 ga gwamnatin tarayya wanda ya ce za a sauke a ranar 13 ga watan Satumba.
Ya kara da cewa JOHESU ta kara ba da wa’adin kwanaki bakwai a ranar Alhamis, 14 ga watan Satumba, 2017 don kara jan hankulin gwamnati zuwa ga bukatun ta.
A cewar shi, babu buri mai ma’ana da aka mora sanadiyan wa’adin.
Josiah ya ce, “ halin rashin kulawar gwamnati ne ya sa kungiyar ta yi kira ga mambobinta na kasa da su janye duk wani hidima su kuma zauna a gida abin da ya kama daga daren yau (Laraba) ko da bayan jiran hakuri har zuwa wannan sa’a kan tabbatar da gyaran CONHESS.\”
Duk da haka, za’a shirya haduwa a harabar asibitoci a kowace rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here