SHUGABA BUHARI YA HALARCI ZAMA DA DONALD TRUMP

0
662
Daga Usman Nasidi
SHUGABAN kasa, Muhammadu Buhari, ya halarci zaman liyafa da shugaban kasan Amurka, Donald Trump, ya shirya wa wasu shugabannin Nahiyar Afrika na musamman a birnin New York.
Shugaba Buhari ya halarci wannan zama a makon jiya, 20 ga watan Satumba bayan mika godiyar da ya yi ga kasar Jordan na makaman da suka taimaka wa Najeriya da shi.
A gefe guda kuma kahegari, shugaban kasa Muahmmadu Buhari yayi wata ganawar hadin kai tare da shugaban kasar Ghana da kuma sarkin Jordan bayan halartar taron majalisar dinkin duniya da shugabannin suka yi a kasar Amurka.
Shugaba Buhari tare da hadiminsa a kan harkokin tsaro Babagana Monguno da ministan harkokin kasashen ketare Geoffry Onyeama, sun yi wata ganawar hadin kai tare da shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo da kuma sarkin kasar Jordan sarki Abdullah na biyu.
Shugabannin sun yi wannan ganawa ne domin hadin kasancen da suke jagoranta da kuma kulla zumunta a tsakaninsu

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here