MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
RESHEN kungiyar Izala ta kasa mai hedkwata Jos da ke Kalaba Jihar Kuros
Riba ya bukaci al’ummar musulmi da su zuba jari wanda babu kamarsa wajen
raya ilmi da kuma karantarwa da karatu.
Alhaji Sale Suleman Jimeta shugaban kungiyar na jihar ne ya bukaci haka lokacin da suka zanta da wakilinmu na kudanci jim kadan bayan da kungiyar ta
gudanar da neman gudunmawar tallafa wa asusun ilmi na kasa na kungiyar
da aka yi.
Shugaban JIBWIS Kuros Riba ya ci gaba da cewa “ka san neman ilimi wajibi
ne ga kowane musulmi zama da jahilci ba hanzari ba ne ga musulmi shi
ya sa ma fadar Allah Madaukakin Sarki Ya ce ku yi karatu ka sanni kafin
ka bauta mini”.Da aka tambaye shi ko mai ya sa JIBWIS ta fi mayar da
hankali wajen fifita gidauniyar neman ilmi alhali ga mabukata irin
matan da aka mutu aka bar musu marayu da kuma ‘yan gudun hijra ana sai
Alhaji Suleman Jimeta ya kara da cewa “ ana yi domin wani lokaci idan
an yi neman taimakon suma ana yi musu ana kuma taimaka musu,amma dai
wannan neman ilmi shi ne mutane suka fi mayar da hankali gare shi galibi
kuma sauran gwamnati kan rika daukar nauyin su”.inji shi.
Akalla kimanin Naira Milyan daya da rabi ake fata a samu gudunmawa a ba
asusun raya ilmi da ilmantarwa na kungiyar daga Jihar Kuros
Riba.Karshe ya nemi al’ummar musulmi da su fito su taimaki Musulunci da
musulmi domin daukakarsa da komai kankantar abin da Allah Ya huwace wa
mutum ba sai lallai mutum ya bayar da wasu makudan kudi ba.Ya yi
addu’ar Allah ya kara wanzar da zaman lafiya a Nijeriya.