Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
LABARIN da ke iske mu daga Jihar Katsina na cewa wadansu masu satar jama\’a sun yi awon gaba da matar mai ba Gwamnan Jihar Katsina shawara a kan harkokin samar da kyakkyawar dangantaka da gwamnati Dakta Lawal Bagiwa.
Masu satar mutanen sun aikata aikin nasu ne ga Hajiya Binta Mainasara Bugaje a kan Titin Kaduna zuwa Zariya a kusa da Jaji
Kamar yadda majiyarmu ta bayyana cewa Bagiwa ya tabbatar da faruwar lamarin kuma wadanda suka sace matar sun yi magana da su amma ba su nemi komai ba ya zuwa yanzu.