MASU GARKUWA SUN SAKO UWARGIDAN HADIMIN GWAMNA MASARI DA SUKA SACE

0
781
Daga Usman Nasidi
A labarin da ke zo wa ma majiyarmu ta Katsina Post yanzun nan na nuni da cewa matar mai bai wa Gwamna Masari shawara a kan lamuran harkallar gwamnatoci Dakta Lawal Bagiwa ta kubuta.
Babban mai taimaka wa Gwamnan a kan kafafen sadarwar zamani Alh Abdulhadi Ahmad Bawa shi ne ya wallafa kubutar matar a shafinsa, sai dai bai bayyana yadda matar ta kubuta ba, wajen sai da aka bayar da kudin fansa ko a’a.
Allah cikin ikonShi da buwayarShi Ya kubutar da Hajiya Binta Bagiwa ( Matar Dakta Lawal Bugiwa) daga hannun wadanda suka yi garkuwa da ita.
A ranar Talata ne dai aka samu rahoton cewa masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da uwargidan mai bai wa Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina shawara a kan harkokin da suka shafi gwamnatocin jiha da jiha Dakta Lawal Bagiwa.
Allah Ya kare duka al\’umma daga sharri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here