MUSA MUHAMMAD KUTAMA, Daga Kalaba
SHUGABAN kwamitin tsaro hadin kai da kuma zama lafiya a Kuros Riba a
turance PSU&P. Alhaji Ya’u Isma’il Girei ya bayar da tabbacin
kwamitinsa zai zage damtse domin ganin matasan Kuros Riba musamman
‘ya’yan ‘yan arewa mazauna jihar kwata ba su shiga harkoki da za su rika
zubar da mutuncinsu da na iyayensu a duk fadin jihar.
Alhaji Isma’il Gorei ya furta haka ne a jawabin marhabun lale da ya yi
lokacin da wakilan kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar
karkashin jagorancin babban darakta a ma’aikatar Mista Emmanuel
B.Ekpenyong da mataimakiyarsa uwargida Immaculata E. Ekpenyong suka
kawo wa kwamitin ziyarar gani da ido a ofishin kwamitin da ke layin
Bagobiri,Unguwar Hausawa da ke Kalaba fadar gwamnatin jihar.
Haka nan kuma shugaban PSU&P ya ci gaba da cewa “mun kafa wannan
kwamiti ne domin tarbiyartar da ‘ya’yanmu da nufin hana su shiga
nau’o’in tsageranci, kungiyanci da makamantan duk wani aiki da zai
haddasa husuma da kuma mu hada hannu da gwamnatin jiha da ta tarayya
wajen bayar da gudunmawa wajen tsaro saboda larura ce ba ta gwamnatin
jiha ko tarayya ba, a’a sai domin magance kalubalen tabarbarewar tsaro
da galibi ya zama ruwan dare a duniya”.inji shi.
Alhaji Ya’u Girei ya kuma bayyana gamsuwarsa matuka gaya yadda ya lura
matasa da suke zuwa daga jihohin arewacin rani suka rungumi sana’a.
Ya ce “ Ina matukar farin ciki musamman ma idan na ga ‘yan uwanmu ‘ya’yan
mu matasa da suke zuwa cin rani suna neman arziki ba su shiga harkokin
kungiyoyi da kuma harkoki na shaye-shaye domin za mu ci gaba da daukar
mataki na ganin mun dakile duk wata harka ta shaye-shaye da masu zuwa
suna bata mana unguwa”.Daga nan ya gargadi matasa da su guji sayen
kayan sata da kuma saye da sayar da kayan maye domin duk wani wanda
aka kama zai dandana kudarsa. Idan an samu mutum da laifi babu ruwan
kwamaitinsa da shi .
A jawabin nasa shugaban ya karkare da yi wa duk masu neman haddasa
husuma da sunan raba kasa cewa kowa ya yi hakuri tun da Allah ya hada mu
kasa daya muzauna tare fitina ba ta da wani amfani kowa ya yi kokarin
zama mutumin kirki shi ya fi.
Da yake mayar da jawabi, jagoran tawagar Mista Emmanuel Effiong a
madadin kwamishinan cewa ya yi “a gaskiya mun gamsu da yadda muka zo
muka ga ashe hadda shugabann addini da sarakuna jagoran wannan kwamiti
mun ga ashe akwai liman da sarki a ciki ai dama tun da sakataren wannan
kwamiti Alhaji Sha’aban Abdullahi ya zo neman izinin gwamnati ta yi wa
wannan kwamiti rajista muka ce babu wata damuwa, muka ji rajistar da za ta
kai shekara biyu kafin ta kare a sake sabuntata ganin wadannan manyan
mutane masu kima da mutunci da muka gani mun san babu wata
tababa”.inji shi.
Har wa yau kwamishinan ya kara da cewa “ mun ji dadin yadda kuka shigo
domin taya mu bayar da gudunmawa wajen harkar tsaro ai mu dama Jihar
Kuros Riba jiha ce ta zaman lafiya, ba kuma za mu taba bari wani ya zo
daga wata jiha ko yanki ba ya cusa mana wata akida ta daban ba. Kuma
Hausawa kuna da tarihin zama Kuros Riba mai kyau domin ba a taba samun
ku ko hannunku a wani yamutsi ba, mun gode da kuka shigo wajen taya
mu tsaro da zaman lafiya”.
Ita kuwa kallabi tsakanin rawuna a taron uwargida Immaculata Ekpenyong,wadda take kula da horar da matasa a ma’aikatar, da ta mike bayan ta yi wa al’ummar arewar da shugabannin kwamitin godiya, matukar farin ciki ta nuna na ganin “ko da muka shigo zauren taron nan hankalina ya fi karkata kan matasa na kuma gan su
wannan ya dada tabbatar mana cewa kun rungumi matasa ba za ku taba bari
su yi zaman banza ko zama bata gari ba. Ta ce “nan gaba gwamnati a shirye
take idan za ta yi wa matasan jihar wata bita ko horo na koyar da sana’o’i,
ma’aikatarmu za mu rubuto wa wannan kwamiti ya ba mu matasa da za mu
hada su da namu a horas da su ko a koya musu sana’a”.
Sai dai kuma Immaculata, ta shawarci kwamitin da ya shigar da ’yan asalin jihar
da ke zaune cakude da ‘yan arewa a unguwar tasu kuma da a guji daukar
doka a hannu da zarar wata matsala ta samu ku rika sanar wa ofishin nasu .
Bayan da mataimakiyar ta gama jawabinta cikin farin ciki tare da
murna ta bayar da dama ko idan akwai wani mai neman karin bayani ko
tambaya, nan take kuwa Alhaji Sani Baba Gombe sarkin Nasarawa/Bacoco
gari na ‘yan arewa tsantsa da ke karamar hukumar birnin Kalaba ya
tambayi kwamishiniyar cewa “mu da aka haife mu a Kuros Riba, mu ma muka
haifa ko mene ne ya sa ba a ba mu satifiket na zama dan kasa wato
indigene certificate da kuma rika daukarmu aikin gwamnati a mataki na
jiha, tun da nan muka yi karatu akwai mu, yaranmu da suka gama manyan
makarantu da kuma jami’o’i “?.
Immaculata Ekpenyong, ta bai wa Alhaji Baba Gombe da amsa da cewa, “dan
uwana magana ta gaskiya mu a nan Kuros Riba ba za mu iya daukar muku
alkawari ba na rika dukar ku aiki ba a matakina gwamnatin jiha, na san
ana tafiya da ‘yan arewa a gwamantin jiha ana nada maku shugaban
hukumar alhazai da kuma ba ku damar nada sarakunanku, kana kuma a
wannan gwamnati, an nada muku mai ba Gwamna shawara kan bakin da ba ‘yan
asalin jiha ba (na musamman), shawarar da zan ba ku a nan ita ce ku rika
nema musu ta fuskar tarayya idan an kawo wani babban ma’aikaci na
tarayya, ku rika mika musu bukatunku, za su taimaka, hanya mafi sauki ke
nan .,
Game da batun katin shaidar zama dan asalin jihar kuwa cewa ta yi
“ A gaskiya wannan matsala ruwan dare ce a Nijeriya, akwai dan uwana
mazaunin Kano ne can ma ya hayayyafa idan wani abu ya taso na karatun
‘ya’yansa shi ma gida Kuros Riba yake dawowa yana musu, ba zan yi karya
ba domin a so ni”.injita.