WASU LAUYOYI SUN SHIGAR DA KARA 17 A KOTUNA DANGANE DA IBRAHIM MAGU

0
689
Daga Usman Nasidi
KIMANIN kara 17 aka gabatar a gaban kotu daban-daban a fadin kasar game da kujerar shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), Malam Ibrahin Magu.
Wasu daga cikin karar na bukatar cire Ibrahim Magu ko kuma a tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar EFCC.
Duk da yake wasu daga cikin karar suna bukatar tabbatar da Magu yayin da mafi yawansu ba su yarda a tabbatar da shi ba.
Daga cikin wuraren da ake samu jinkirin al’amuran sun hada da babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja da ta Yola a jihar Adamawa da ta Kano a jihar Kano da kuma Legas.
Game da karar 7 suna jira a gaban babbar kotu ta Abuja, yayin da sauran 12 suka kasance a wasu sassa uku.
Wasu lauyoyi da kungiyoyi suka gabatar da mafi yawan wadannan karar. Wani babban lauya na Abuja, Johnmary Jideobi ya gabatar da daya daga cikin karar yayin da yake neman umarnin kotu don dakatar da Magu daga bayyana kansa a matsayin shugaban EFCC.
Wani lauya na Abuja, Wale Balogun shi kuma ya na neman kotun ta dakatar da Magu daga ci gaba da zama shugaban hukumar.
Wani lauya daga Legas, Ebun-Olu Adegboruwa, shi ma ya gabatar da kara a kan Magu, amma daga bisani sai ya janye karar.
Har ila yau, wasu kungiyoyi biyu, Save Nigeria Group da kuma kungiyar kare hakkin dan Adam wato Kingdom Human Rights Foundation sun gabatar da kara game da Magu, amma daga bisani suka janye.
Duk da haka, ministan shari\’a, Abubakar Malami (SAN), ya bukaci babban alkali na kotun tarayya, Abuja, Justice Abdul Kafarati ya sulhunta tsakanin kara 17 da aka shigar don kauce wa yin shara’a daban-daban a karkashin ikon kotun.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here