Rabo Haladu Daga Kaduna
GWAMNATIN Najeriya ta yanke shawarar ficewa daga wasu kungiyoyin kasa da kasa kusan 90,
sakamakon dawainiyar da ke tattare da mu`amala da kungiyoyin.
Majalisar zartarwar kasa ce ta dauki wannan matakin, tana cewa bashin kudin gudummuwar
raya kungiyoyi kadai da ake bin gwamnatin ya zarta Dala Miliyan 100.
Mai taimaka wa shugaban kasa a kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya
shaida wa manema labarai cewa, akwai kungiyoyi birjik ko na tsakanin kasa da kasa ko na Majalisar Dinkin
Duniya ko kuma na kungiyar hadin kan Afirka da Najeriya ta shiga cikinsu wadanda kuma
dukkansu akwai bukatar gudummuwar da duk kasar da ke cikinsu sai ta bayar a karshen
kowacce shekara.
Malam Garba Shehu, ya ce saboda irin wadannan kudaden gudummuwar tafiyar da kungiyoyin
wadanda Najeriya ba ta biya ba, har ta kai idan aka je taro akan bukaci mai wakiltar Najeriya da ke
wajen ya fita, saboda kawai ana bin kasarsa bashin kudin gudunmmuwar kungiyar. Ya ce hakan ba karamin abin kunya ba ne ga Najeriya.
Don haka shugaba Muhammadu Buhari ya ce, to ya kamata a sake lale, inda za a baje irin wadannan kungiyoyin a faifai a zabi wadanda ke da amfani ga kasar dan a ci gaba da tafiya tare da su.
Kakakin shugaban Najeriyar, ya kara da cewa wasu basussukan da ake bin Najeriyar ma, wani ko
shugaban kasa ko kuma minista ne zai je tarukan irin wadannan kungiyoyi ya yi alkawarin
cewa, ai Najeriya za ta bayar da gudunmuwar kaza wanda kudin ma babu su a kasa. Ya ce: \’\’To irinsu ne suka taru suka yi wa Najeriya yawa, har ta kai ana kunyata ta a wajen taro.\’\’
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce a wannan bangare, gwamnatinsa za ta dauki iya abin da take ganin za ta iya ne wajen mu\’amala da irin wadannan kungiyoyi.
Malam Garba Shehu, ya ce wadannan basukan ma da aka ce ana bin Najeriyar, tun na shekara da shekaru ne, don haka a kididdige shi ma abu ne mai kamar wuya.
Haka kuma ya yi nuni da cewa, ba matsi ne ya sa Najeriya za ta fice daga wadannan kungiyoyi ba,
sanin ciwon kai ne kawai.