FARASHIN MASARA DA SHINKAFA YA FADI A KASUWAR HATSI TA GARIN SAMINAKA  

0
1446

Isah  Ahmed, Jos  

SAKAMAKON shigowar kaka da kuma irin dibbin  noman da al’ummar kasar nan suka yi a daminar bana, ya zuwa yanzu farashin kayayyakin amfanin gona kamar masara da shinkafa ya fadi kasa,  a babbar kasuwar hatsi ta garin Saminaka dake jihar Kaduna. Shi dai yankin na  Saminaka da ke jihar Kaduna ya yi suna wajen noman masara  da sauran kayayyakin amfanin gona a Nijeriya.

Binciken da wakilinmu ya gudanar a wannan kasuwa ya gano cewa a yanzu ana sayar da buhun sabuwar masara da ta bushe, kan kudi naira dubu 7, a yin da  ake sayar da buhun tsohuwar masara kan kudi naira dubu 8, maimakon naira dubu 15 da ake sayarwa a kwanakin baya.

Har’ila yau wakilin namu ya gano cewa yanzu ana sayar da buhun shinkafa mai bawo kan kudi naira dubu 8 maimakon naira dubu 12 da ake sayarwa a kwanakin baya.

Hakazalika wakilin namu ya ganewa idonsa yadda baki masu sayen kayayyakin amfanin gona daga wurare daban daban suka cika wannan kasuwa ana ta loda kayayyakin amfanin gona a motoci. Wasu masu sayen kayayyakin amfanin gonar da wakilin namu ya zanta da su, sun bayyana matukar farin cikinsu kan yadda kayayyakin amfanin gonar ya cika kasuwa kuma a  farashi mai rahusa.

A zantawarsa da wakilinmu Sarkin hatsi na babbar kasuwar hatsin ta garin Saminaka Malam Manu Isah Idris ya bayyana cewa su babu abin da zamu ce sai dai su yiwa Allah godiya, kan ganin wannan  kaka.  Ya ce babban dalilin da ya kawo faduwar farashin na masara shi ne shigowar kaka da kuma  jita-jitar cewa akwai kamfanonin da suka shigo da masara daga waje.

 Ya yi  kira ga manoman  suyi taka tsantsan wajen kawo kayayyakin amfanin gonarsu kasuwa a yanzu, saboda kusan duk manomin da ya kawo kayan amfanin gonarsa kasuwa yana faduwa ne.

Har’ila yau ya yi kira ga gwamnati kan ta kara tallafa wa manoma domin tallafawa manoma  ne zai magance rashin aikin yi a kasar nan. Ya ce yanzu kusan dukkan mutanen da suke yankunan karkara sun sami aiki ta hanyar rungumar aikin gona. Don haka gwamnati ta kare amfanin gonar da manoma suka noma, kuma ta hana shigo da duk wani amfanin gona zuwa kasar nan,  yin haka ne zai sanya mutane su kara rungumar aikin noma a kasar  nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here