MASU SON MULKI NE SUKE KIRAYE-KIRAYEN A SAKE FASALIN NIJERIYA-FARFESA DADARI  

0
799
 Isah Ahmed, Jos
 
WANI malami a sashin bincike da koyar da dabarun noma na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum Farfesa Salihu Adamu Dadari ya bayyana cewa duk masu kiraye-kirayen a sake fasalin kasar nan, mutane ne masu kwadayin mulki. Farfesa Salihu Adamu Dadari ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
 
Ya ce Nijeriya a tsare take, mutane ne suka ba ta tsarin ta hanyar cin hanci da zalunci da son zuciya.
‘’Ko za a sake fasalin Nijeriya sau 100 matukar akwai cin hanci da rashawa da son zuciya aikin banza ne. Yaki da cin hanci da rashawa  ne mafita ba sake fasalin Nijeriya ba. Mu sadaukar da kanmu ga Nijeriya mu yaki cin hanci da rashawa ne mafita a Nijeriya’’.
 
 
Farfesa Dadari ya yi bayanin cewa ba a abin mamaki ba ne da aka ce kasar Faransa tana mara wa kungiyar neman kasar Biyafara ta [IPOB] Ya ce dama an danganta kasar Faransa da boko haram.
 
Ya ce kasar Faransa tana cikin manyan  kasashen duniya na G7 wadannan kasashe  a kullum ba kasar da ta tsole masu ido a Afrika, kamar  Nijeriya.  Domin Allah ya yi mata albarka na kowanne al’amari na rayuwa tun daga albarkatun kasa kamar  fetur da noma da mutane masu hazaka. Don haka  Faransa za ta iya yi wa Nijeriya komai, da zai kawo mata cikas.
 
‘’Wadannan kasashe na G7 sun nuna cewa Nijeriya za ta wargaje a shekara ta 2015. Yau ga shi har yanzu Nijeriya tana nan a dunkule. Don haka idan Faransa ta bai wa Nnamdi Kanu kudi don ya zo ya wargaza Nijeriya ba a abin mamaki ba ne’’.
 
Ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta yi wa Nnamdi Kanu mummunan hukunci kan cin amanar kasa da ya yi tare da masu daure masa gindi.
 
 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here