Rabo Haladu Daga Kaduna
ANA ci gaba da aikin nemo mutane da daman da
suka nutse a cikin wani kogi sakamakon
hatsarin jirgin ruwan fasinja lokacin da suke kan
hanyarsu cikin karamar hukumar Yawuri a jihar
Kebbi.
Rahotanni sun ce jirgin ya taso ne daga kauyen
Jalbabu, inda ya nufi zuwa Yawuri dauke da
fasinjojin da ake tsammanin adadinsu ya kai 50
zuwa 60.
Shugaban karamar hukumar Yawuri, Alh Musa
Muhammad, ya shaida wa manema labarai cewa, ya zuwa
maryace an gano tare da yi wa
gawawwakin mutum 15 jana\’iza.
A cewarsa wasu daga cikin mutanen da ke cikin
jirgin sun kubuta amma akwai wasu da dama
wadanda har yanzu ba a iya gano su don haka
ake ci gaba da bincike fasinjojin da ake kyautata
tsammanin suna cikin ruwa.
Ya ce, jirgin ya yi hatsari ne sakamakon karo da
wani kututture a tsakiyar kogi, lamarin da ya sa
ya tsage sai kuma mutanen da ke ciki suka
tsorata daga nan jirgin ya kife da su.
Ko a cikin watan jiya ma, wani hatsarin jirgin
ruwa a karamar hukumar Bagudo ta jihar Kebbin
ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 50 a cikin
kogin Neja.
Musa Muhammad ya ce wasu daga cikin
fasinjojin da ke jirgin, sun samu fitar da kansu,
wasu kuwa sai da aka taimaka musu saboda ba
su iya ninkaya ba.
Ana danganta aukuwar hatsarin jiragen ruwa da
cunkoson da ake yi musu, ta hanyar daukar
mutane da kaya fiye da kima da kuma rashin
yashe kogunan da ake sufuri a cikinsu.
Shugaban karamar hukumar Yawurin, ya ce
yanzu ana wayar da kan direbobi jiragen ruwa kai
a yankinsa, game da muhimmancin bin ka\’ida
wajen daukar mutane, sannan su tabbatar da
lafiyar jiragensu a kowanne lokaci.