Zaki Ya Kashe Mai Kula Da Shi A Ibadan

0
799

Rabo Haladu Daga  Kaduna

HUKUMOMIN kasar nan sun rufe wani gidan
namun daji (Zoo) bayan wani zaki ya kashe
wani ma\’aikacin gidan.
Al\’amarin ya faru ne a gidan Zoo na Agodi a
makon jiya a Jihar Oyo kamar yadda gwamnatin jihar
ta tabbattar.
Marigayin mai suna Hamzat Oyekunle ya mutu
ne sanadiyyar raunin da ya ji yayin da zakin ya
kai masa hari.
Rahotanni sun ce marigayin ya kwashe \”tsawon
shekara biyar yana ciyar da zakin kuma ya saba
da dukkannin dabbobin da ke gidan Zoo din.\”
Gwamnatin jihar wadda ta bayyana rashin jin
dadinta kan al\’amarin ta ce an fitar da zakin
daga gidan Zoo din yayin da ake ci gaba da bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here