Bikin Ranar Malamai Bai Yi Armashi Ba a Jihar Adamawa

0
698

Rabo Haladu Daga Kaduna

BIKIN ranar tunawa da malamai a jihar Adamawa, malaman  jihar ba su ji dadin ranar ba saboda har yanzu gwamnati ba ta biya su kudadensu ba, haka kuma dakunan karatun yara wasunsu kamar dakunan awakai suke bikin wannan shekara na “Ranar Malamai Ta Duniya” da Asusun Kula Da Yara na Majalisar Dinkin Duniya yakan shirya a kowace ranar biyar ga watan Oktoba don yin juyayin halin da harkar ilimi take ciki
da aka gudanar a jihar Adamawa bai yi armashi ba saboda abin da da malaman suka kira alkawurran romon baka da gwamnatin ke yi amma ba ta cikawa a duk zagayowar wannan rana.
Wasu malamai da suka halarci bukin tunawa da ranar wadda aka kaddamar a Dandalin Mahmud Ribadu da ke Yola, fadar jihar, sun bayyana rashin fitowar malamai musamman na matakin firamare da rashin tasirin sa a rayuwarsu a kan matsalolin da suke fuskanta, da suka hada da bashin albashin wattani uku da suke bin gwamnati, da kudin alawus na hutu na shekaru biyar, ga shi kuma rabon da a yi wa malamai karin girma tun shekarar 2002.
Mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Marthins Nasiru Babale ya shaida wa taron malaman cewa gwamnati na nazarin yadda za ta magance matsalolinsu, kana ya yi anfani da ranar wajen kira a kan kanfanoni,
masana’antu, kungiyoyi da mutane masu hannu da shuni su taimaka wa gwamnati wajen farfado da harkar ilimi.
Sai dai kalaman, ga alamu, ba su yi wa malaman dadi ba, da yake suna tsammanin cewa gwamnati za ta shata jaddawalin magance matsalolin nasu.
Da yake wa manema labarai bayani a kan sakon “Ranar Malamai Ta Duniya” na bana mai taken ‘biyan
hakkokin malamai da samar da yancin karantarwa cikin walwala da tsaro,
Shugaban Kungiyar Malamai Ta Najeriya reshen jihar Adamawa, Komrad Rodney Nathan ya ce fatar
kungiyar ce ta ga ranar da gwamnati za ta cika alkawurran da ta sha dauka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here