Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABAN hukumar kwastan Kanar Abdulhamid Ibrahim Ali, ya bayyana cewa nan da watanni uku masu
zuwa hukumar za ta matukar takaita fasa kwauri domin kare manufofin noma a kasa .
Shugaban hukumar kwastan ta kasa ya bayyana cewa hakkin su ne su tabbatar cewa manoma sun amfana daga shirye-shirye da tsare-tsaren gwamnati kan harkokin noma.
Wadannan maufofi batu ne na noman shinkafa hakazalika shi ma fasa kwaurin duk a kan harkokin shinkafa ne. Gwamnatin tarayyar ta mayar da hankali sosai a kan nomanshinkafa domin yanzu haka babban bankin Najeriya, na shirye shiryen taimaka wa manoma shinkafa kimanin miliyan goma sha biyu.
Malam Shu’aibu Mungadi, mai sharhi ne kan al’amurran yau da kullum ya bayyana cewa babban kuskure ne idan gwamnati ta mayar da hankali wajen habaka noman shinkafa kadai, domin kuwa a cewar sa, kowane bangare na kasar na da irin amfanin da suke nomawa, dan haka wajibi ne a tallafa wa dukkan nau’ukan noma, banma shinkafa kadai ba.
Kwararre kan harkokin noma Alhaji Musa Ibrahim, kuma ya bayyana cewa a ganinsa dalilin da ya sa gwamnati ta mayar da hankali kan noman shinkafa shi ne domin ita ce mafi akasarin amfanin gonar da ake shigowa da ita daga kasashen ketare.
Ya kuma kara da cewa idan gwamnati za ta fadada noman zuwa ga su alkama, waken suya da noman rogo tund ana flawa da sitaci da shi, da sauran abubuwa daban-daban da kuma samar da kananan masana’antu domin sarrafa kayayyakin goma, ta haka ne kawai hakarta za ta cimma ruwa.