Ana Zargin Wata Matar Aure Da kashe Mijinta A Kwantogora

0
865

Rabo Haladu Daga Kaduna

IYALAN wani magidanci mai suna Danlami Abdullahi, da aka fi sani da suna Dan Hajiya, na zaman makomi a garin Kontogora na jihar Neja, a sakamakon rasuwar da ya yi ta sanadiyyar murde masa mazakuta da ake zargin matarsa ta yi masa.
Bayanai sun nuna cewa an sami sabani ne a tsakanin marigayin da matarsa mai suna Rahanatu Abdullahi, wadda suka kwashe tsawon shekaru Takwas suna tare a matsayin miji da mata har ma da ‘ya’ya uku, lamarin ya faru ne ta sanadiyyar karin aure da ya ce zai yi amma wadda ake zargin ta musanta.
Hajiya Kande Ahmad, mahaifiya ce ga marigayin kuma ta bayyana cewa ta iske su a sa’ilin da suke fada da juna, ta kara da cewa marigayin ya bayyana mata cewa matar tasa na rike da
gabansa, kuma ta ki saki sai da ya yi kuwwa domin neman dauki daga jama’a.
Muhammadu Sani Usman, da ke zaman dan’uwan marigayin ya bayyana cewa yayin da suka je asibiti, marigayin ya bayyana masa cewa ciwon zuciya  ke damunsa.
Manema labarai sun sami jin ta bakin matar marigayin wadda ta bayyana masu cewa babu kamshin gaskiya a cikin maganar domin a cewarta mahaifiyarsa na kokarin kare shi ne kawai.
Rundunar ‘yan sadan jihar ta bayyana cewa ba ta da masaniya a kan afkuwar lamarin amma ta bayyana cewa za ta fara bincike kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here