Ba Ni Da Niyyar Tsayawa Takara A 2019 — Osinbajo

0
736

Rabo Haladu Daga Kaduna

MATAIMAKIN Shugaban kasa  Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce bai taba tunanin zai tsaya takarar shugabancin kasa ba a zabe mai zuwa na shekarar 2019, ba shi kuma da lokacin da zai yanke wannan shawarar.
Mataimakin shugaban kasar a wani taron kasashen Afirka a London yana cewa: \’Babu wannan tunanin cikin tsarina.\”
Akwai rashin tabbas sosai a kasar kan ko shugaba Muhammadu Buhari yana da aniyar sake tsayawa takara a 2019.
Shugaba Buhari ya karbi mulkin  a shekarar 2015, sai dai ana ganin bai cika karsashi wajen tafiyar da kasar yadda aka za ta ba, saboda yawan rashin lafiyar da yake fama da ita.
A lokutan da shugaban ke jinya a London, an sha rade-radin cewa ko akwai sabani a tsakaninsa da
mataimakin nasa Farfesa Osinbajo, sai dai an kasa gasgata hakan ganin yadda yake mika masa
ragamar tafiyar da kasar a duk lokacin da baya nan.
Kazalika, a wajen taron Farfesa Osinbajo ya kuma ce a yanzu masu tayar da kayar baya na Neja-Delta ba sa yin wata barazana kan samar da man fetur a yankin.
Ya ce: \”Ba za mu ci gaba da amfani da fetur har abada ba, don haka dole mu yi amfani da fetur a lokacin da yin hakan ke da ma\’ana.\” Najeriya dai ta dade tana dogaro da man fetur din da take da shi wajen tafiyar da al\’amura kasar, sai dai masu sharhi na ganin lokaci ya yi da ya kamata ta daina hakan don ganin nan gaba za a rage amfani da man fetur a duniya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here