Gwamna El-Rufa\’i Na Tare Da Karamar Hukumar Kauru Dalilin Jajircewarsu A Zaben Buhari

0
789

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

GWAMNAN Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa\’i ya rungumi jama\’ar karamar hukumar Kauru ta hanyar bayar da kujerar babban kwamishina ga Ya\’u Shehu Usman Kauru wanda dan asalin karamar hukumar ne.

Nasiru Ahmad El-Rufa\’i ya bayyana karamar hukumar Kauru a matsayin karamar hukuma kwaya daya rak da ta samu nasarar kawo zaben shugaban kasa a yankin kudancin Jihar Kaduna a zaben da ya gabata.

Gwamna El-Rufa\’i ya bayyana cewa a duk lokacin da ya hadu da shugaba Buhari yakan tambaye shi mene ne  ya yi wa Kauru?

\”Don haka a yanzu zan samu bakin maganar abin da na yi wa karamar hukumar, yanzu zan je Abuja za mu yi taro da wasu Gwamnoni kuma zan gaya wa shugaban kasa abin da na yi wa mutanen Kauru na nada dansu a matsayin kwamishinan da ba zan iya cirewa ba sai mun kai wa majalisa domin karfin su\”.

Gwamnan dai ya zabo Ya\’u Shehu Usman Kauru ne saboda nagartarsa a fannin aikin gwamnati musamman a bangaren kudi.

Ita dai wannan hukuma za ta yi aikin saka idanu ne ga duk wanda ke kokarin barnatar da dukiyar jama\’a ko ni kaina Gwamnan suna da \’yancin bincikena idan aka same ni da matsala a kan harkar kudi.

Su dai wadanda aka nada sun hada da Buhari Gani kashe ni Aliyu Yahya Sa\’ad, Lawal Dan Ladi da Sa\’adatu Balarabe Mahmud a matsayin kwamishinoni yayin da Ya\’u Shehu Usman Kauru yake a matsayin shugaban hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here