Matasa Su Ne Kashin Bayan Kowace Al\’umma

0
828

MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba

SHUGABAN kwamitin tsaro hadin kai da kuma zama lafiya a Kuros Riba a turance PSU&P. Alhaji Ya’u Isma’il Girei ya bayar da tabbacin kwamitinsa zai zage damtse domin ganin matasan Kuros Riba musamman ‘ya’yan ‘yan arewa mazauna jihar kwata ba su shiga harkoki da za su rika zubar da mutuncin su da na iyayensu a duk fadin jihar ba.

Alhaji Isma’il Girei ya furta haka ne a jawabin marhabun lale da ya yi lokacin da wakilan kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar karkashin jagorancin babban Darakta a ma’aikatar Mista Emmanuel B.Ekpenyong da mataimakiyarsa uwargida Immaculata E. Ekpenyong suka kawo wa kwamitin ziyarar gani da ido a ofishin kwamitin da ke Layin Bagobiri, Unguwar  Hausawa da ke Kalaba fadar gwamnatin jihar.

Haka nan kuma shugaban PSU&P ya ci gaba da cewa “mun kafa wannan kwamiti ne domin tarbiyartar da ‘ya’yanmu da nufin hana su shiga nau’o’in tsageranci, kungiyanci da makamantan duk wani aiki da zai haddasa husuma da kuma mu hada hannu da gwamnatin jiha da ta tarayya wajen bayar da gudunmawa wajen tsaro saboda larura ce ba ta gwamnatin jiha ko tarayya ba a’a sai domin magance kalubalen tabarbarewar tsaro da galibi ya zama ruwan dare a duniya”.

Alhaji Ya’u Girei ya kuma bayyana gamsuwarsa matuka gaya yadda ya lura matasa da suke zuwa daga jihohin arewa cin rani suka rungumi sana’a. Ya ce “ Ina matukar farin ciki musamman ma idan na ga ‘yan uwanmu ‘ya’yanmu matasa da suke zuwa cin rani suna neman arziki ba su shiga harkokin kungiyoyi da kuma harkoki na shaye-shaye domin za mu ci gaba da daukar mataki na ganin mun dakile duk wata harka ta shaye-shaye da masu zuwa suna bata mana unguwa”.Daga nan ya gargadi matasa da su guji sayen kayan sata da kuma saye da sayar da kayan maye domin duk wani wanda aka kama zai dandana kudarsa. Idan an samu mutum da laifi babu ruwan kwamaitin sa da shi .

A jawabin nasa shugaban ya karkare da yi wa duk masu neman haddasa husuma da sunan raba kasa cewa kowa ya yi hakuri tun da Allah ya hada mu kasa daya mu zauna tare fitina ba ta da wani amfani kowa ya yi kokarin zama mutumin kirki shi ya fi.

Da yake mayar da jawabi jagoran tawagar Mista Emmanuel Effiong a madadin kwamishinan cewa ya yi “a gaskiya mun gamsu da yadda muka zo muka ga ashe hadda shugaban addini da sarakuna jagoran wannan kwamiti mun ga  ashe akwai liman da sarki a ciki ai dama tun da sakataren wannan kwamiti Alhaji Sha’aban Abdullahi ya zo neman izinin gwamnati ta yi wa  wannan kwamiti rajista muka ce babu wata damuwa muka ji rajistar da za ta kai shekara biyu kafin ta kare a sake sabunta ta ganin wadannan manyan mutane masu kima da mutunci da muka gani mun san babu wata tababa”.injishi.

Har wayau kwamishinan ya kara da cewa “ munji dadin yadda kuka shigo domin taya mu bayar da gudun mawa wajen harkar tsaro ai mu dama jihar Kuros Riba jiha ce ta zaman lafiya ba kuma za mu taba bari wani ya zo daga wata jiha ko yanki ba ya  cusa mana wata akida  ta daban ba kuma Hausawa kuna da tarihin zama kuros riba mai kyau domin ba,a taba samun ku ko hannun ku a wani yamutsi ba, mun gode da kuka shigo wajen taya mu tsaro da zaman lafiya”.

Ita kuwa kallabi tsakanin rawuna a taron uwargida Immaculata Ekpenyong,wadda take kula  da  horar da matasa a maaikatar   da ta mike bayan tayiwa al’ummar arewar da shugabannin kwamitin godiya matukar farin ciki ta nuna na ganin “koda muka shigo zauren taron nan hankalina ya fi karkata kan matasa na kuma gansu wannan ya dada tabbatar mana cewa kun rungumi matasa ba za ku taba bari su yi zaman banza ko zama vata gariba ta ce “nan gaba gwamnati a shirye take idan zatayiwa matasan jihar wata bita ko horo na koyar da sana’o’i ma’aikatar su za mu rubuto wa  wannan kwamiti ya bamu matasa da za mu hada su da namu a horas da su ko a koya musu sana’a”.Sai dai kuma Immaculata, ta shawarci kwamitin da ya  shigar da ,yan asalin jihar da ke zaune cakude da ‘yan arewa a unguwar tasu kuma da a guji daukar doka a hannu da zarar wata matsa ta samu ru rika sanar wa ofishinsu .

Bayan da mataimakiyar ta gama jawabin ta cikin farin ciki tare da murna ta bayar da dama ko idan akwai wani mai neman karin bayani ko tambaya nan take kuwa Alhaji Sani Baba Gombe sarkin Nasarawa/Bacoco gari na ‘yan arewa tsatsa dake karamar hukumar birnin Kalaba ya tambayi kwamishinar cewa “mu da aka haife mu a Kuros Riba,mu ma  muka haifa ko  me ya sa ba a ba mu satifiket na zama  dan kasa wato indigene certificate da kuma rika daukar mu aikin gwamnati a mataki na jiha tun da nan muka yi karatu akwai mu,yaran mu da suka gama manyan makarantu da kuma jami’o’i “?.

Ga amsar da Immaculata Ekpenyong, ta baiwa Alhaji Baba Gombe “dan uwana magana ta gaskiya mu a nan kuros riba ba zamu iya daukar muku alkawari ba na  rika dukar mun aiki ba a matakina gwamnatin jiha nasan ana tafiya da ,yan arewa a gwamantin jiha ana nada maku shugaban hukumar alhazai da kuma baku damar nada saraku nan ku kana kuma a wannan gwamnati ai nada muku mai ba gwamna shawara kan baki daba ,yan asalin jiha ba na  musamman,shawarar d azan baku anan itace ku rika nema musu ta fuskar taraiya idan an kawo wani babban maaikaci na taraiya ku rika mika musu bukatun ku zasu taimaka hanya mafi sauki ke nan .,Game da batun katin shaidar zama dan asalin jihar kuwa cewa tayi “ A gaskiya wannan matsala ruwan dare ce a nijeriya, akwai dan uwana mazaunin Kano ne can ma ya hayayyafa idan wani abu ya taso na karatun ,ya,yan sa shima gida kuros riba yake dawowa yana musu bazan yi karya ba domin a so ni”.injita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here