Isah Ahmed, Jos
SHUGABAN majalisar malamai na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga gwamnonin jihohin Nijeriya su rika ci gaba da ayyukan raya kasa da suka gada daga gwamnonin da suka gabata. Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a garin Jos.
Ya ce ya kamata duk abin da aka fara ginawa kamar hanyoyin mota ko asibitoci ko makarantu duk wanda ya zo ya dora a kan wannan aiki da ya tarar. Kada ya yi amfani da siyasa ya dakile wadannan ayyukan raya kasa da wasu shugabannin baya suka fara.
‘’Duk ayyukan raya kasa da wani gwamna ya zo ya gada ya dora kan wannan aiki ya kammala domin al’umma su amfana. Ba daidai ba ne gwamnoni su rika watsi da ayyukan raya kasa da suka gada, saboda siyasa su Ki ci gaba da gudanar da wadannan ayyuka maimakon su kirkiro nasu’’.
Shiekh Jingir ya yi kira ga gwamnati ta dauki mataki kan masu tallan magunguna suna yin batsa a kasuwannin kasar nan, domin suna maganganun batsa na lalata tarbiyar al’umma.
Ya ce wadannan masu tallar magunguna suna maganganun batsi a cikin unguwanni da kasuwanni. Wannan abu da suke yi daidai ba ne a cikin al’ummarmu, domin suna bata tarbiyar jama’a. Don haka lallai ya kamata gwamnati ta dauki mataki kan irin wadannan mutane, domin suna taimakawa wajen lalata tarbiyar yaranmu.
Daga nan ya yaba wa shugaban kasa Muhammad Buhari kan yadda gwamnatinsa ta jajirce kan tsaro a kasar nan. Ya ce sakamakon kokarin gwamnatin Buhari, yanzu Allah ya rushe mana boko haram kuma an magance masu kokarin raba kasar nan, ta hanyar fafutukar neman kasar Biyafara.