Isah Ahmed, Jos
WANI manomi kuma shugaban kasuwar ‘yan tumatur dake garin Jos babban birnin Jihar Filato Alhaji Aminu Yahaya Yunusa ya bayyana cewa babu shakka matakin da gwamnatin Nijeriya ta dauka, na hana shigo da kayayyakin abinci ta kan iyakokin kasar nan, gata ne take yi wa manoman Nijeriya. Alhaji Aminu Yahaya ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce hana shigo da abinci zuwa cikin kasar nan, manoma ake yi wa gata. Domin idan aka hana shigo da abinci dole ne a rika sayen abincin da manomanmu suka noma da daraja.
Ya ce a duk ran da aka ce manoma suna yin noma, suna yin asara saboda karyewar darajar kayayyakin amfanin gonar da suka noma, za su daina yin noman kamar yadda ya faru a baya, wanda wannan babbar asara ce ga kasa.
‘’Amma ya kamata manoma su lura duk kayayyakin amfanin gonar da suka noma sun noma ne don a sami sauki. Ba sai kayayyakin amfanin gonar ya yi muguwar tsada ba. Amma in son samu ne idan manomi ya yi noma kada ya yi asara. Idan manoma suna cin riba, ba za a daina yin noma ba, a kasar nan’’.
Alhaji Aminu Yahaya ya yi bayanin cewa babu shakka gwamnatin nan ta lura babu abin da ya fi noma mahimmanci a wajen talakawan Nijeriya. Domin shi ne zai iya samarwa da talakawan Nijeriya ayyukan yi. Don haka ta tashi tsaye wajen bunkasa harkokin noman.
Ya ce sakamakon kokarin da wannan gwamnati ta yi, bana mutane da yawa sun rungumi aikin noma a Nijeriya kuma bisa dukkan alamu daga bana mutane za su ci gaba da aikin noma a Nijeriya. Ya ce wannan ba karamin ci gaba ba ne ga al’ummar Nijeriya da gwamnati baki daya. Domin da yardar Allah daga wannan shekara tattalin arzikin Nijeriya zai farfado sakamakon wannan noma da aka yi.
Ya yi kira ga gwamnati ta kara sanya ido kan takin zamani a kasar nan, idan gwamnati ta yi haka kowa zai koma noma a Nijeriya.