Isah Ahmed, Jos
ALHAJI Ibrahim Abdullahi Muhammad Ibzar shi ne shugaban kamfanin dab’i da wallafa na Ibzar Publishing company Ltd da ke garin Jos babban birnin Jihar Filato. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana muhimmancin sana’ar dab’i da wallafa ga al’ummar kasar nan. Haka kuma ya bayyana cewa matakin da ma’aikatar ilmi ta tarayya ta dauka na baiwa kananan kamfanonin dab’i da wallafa na kasar nan ayyukan dab’i da wallafa zai bunkasa wannan sana’a a Nijeriya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-
GTK; Mene ne wannan sana’a ta dab’i da wallafa ta kunsa?
Ibzar; Wannan sana’a tana da tarihi kuma ta kunshi abubuwa masu tarin yawa. Domin an fara wannan sana’a tun karnoni da dama da suka gabata.
Wannan sana’a wadda take da alaka da buga takardu, ta shafi al’umma gabaki daya ta bangarori da dama. Domin babu wata ma’aikata ta gwamnati ko ma’aikata mai zaman kanta, ko makaranta ko wani dan kasuwa ko wani ma’aikaci ko wani dalibi da ba ta shafa ba.
Kuma yanzu abubuwan da aka fi gudanarwa a wannan sana’a su ne buga takardun makarantu, littafai, takadun aure, takardun suna, takardun bukuwa, takardun kiwon lafiya, takardun fastocin ‘yan siyasa, kalandu, rahotannin shekara-shekara, takardun jarrabawar makarantu da dai sauransu.
GTK; Wanne irin muhimmanci ne wannan sana’a take da shi ga al’ummar kasar nan?
Ibzar; ; Babu shakka wannan sana’a tana da matukar muhimmanci ga al’umma kuma tana ba da gudunmawa wajen samar wa da matasa ayyukan yi a kasar nan. Domin a duk inda ka ga ana gudanar da wannan sana’a za ka ga mutane da yawa, suna gudanar da ayyuka daban-daban na wannan sana’a. Saboda tana da bangarori da dama tun daga bugawa zuwa kammalawa. Kuma wannan sana’a tana taimakawa wajen bunkasa harkokin kasuwanci a kasar nan. Tun daga sayen takarda da tawada da sauran sinadarai na aiki. Kadan kenan daga cikin muhimmancin wannan sana’a.
GTK; Wanne hali ne wannan sana’a take ciki a wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari?
Ibzar; A gaskiya wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammad Buhari ta dauko matakai na tallafa wa masu wannan sana’a musamman kananan kamfanonin dab’i da wallafa na kasar nan, har da manya. Domin wannan gwamnati ta bangaren ma’aikatar ilmi ta tarayya wadda ministan ilmi Malam Adamu Adamu yake jagoranta, ya bayar da dama ga dukkan bangarorin ma’aikatar ilmi ta tarayya, wajen ganin sun fadada kwangiloli don shigar da kananan kamfanonin dab’i da wallafa na bangarorinsu, maimakon takura abubuwa wajen ba wasu shafaffu da mai da ba su fi kamfanoni 10 ko kasa da haka ba.
Akalla an bai wa kananan kamfanonin dab’i da wallafa sama da 300 wannan aiki, na buga littafan da ake koyarwa a makarantun firamare da sakandire na kasar nan. Wadannan kamfanoni suna nan suna ci gaba da wannan aiki da aka ba su ta hanyar ‘yan kwangila. Kafin a ba da wannan umarni akwai mawallafa sama da 600, waxanda sun rubuta littafai amma ba a buga su ba, domin ba su da hanyar bugawa. Amma yanzu irin wadannan littafai da aka rubuta suna daga cikin irin ayyukan da aka bai wa wadannan kamfanoni su je su buga su kawo,don a raba a makarantun kasar nan.
Babu shakka wannan mataki da ministan ilmi Mallam Adamu Adamu ya dauka tare da hadin kan babban sakataren hukumar ilmin bai daya [UBEC] Dokta Hameed Bobboyi da sauran ma’aikatansu ya bude kafa ta tallafa wa irin wadannan kananan kamfanoni, wadanda ada ba a yi da su. Kuma wannan mataki ya bai wa irin wadannan kamfanoni dama wajen farfado da harkokinsu tare da ba su dama wajen samar da karin guraben ayyuka ga al’ummar kasar nan. Yanzu idan ka shiga cikin garuruwan Abuja da Kaduna za ka ga wuraren ayyukan buga littatafai da takardu sun cika ana ta ayyuka, sakamakon wannan mataki da aka dauka. Babu shakka wannan abin koyi ne da ya dace sauran bangarorin gwamnati su dauka a matsayin kalubale.
Don haka muna godiya ga wannan gwamnati, domin ba a taba samun gwamnatin da ta tallafa wa kananan kamfanonin dab’i da wallafa kamar wannan gwamnati ba. Domin a gwamnatocin da suka gabata ba a maganar irin wadannan kamfanoni, sai manya kadai.
Babu ma’aikatar gwamnatin da babu wurin da masu dab’i da wallafa da ba za su yi mata aiki ba. Yin haka zai dada bunkasa wadannan kananan kamfanoni kuma za a sami ayyukan yi da yawa a wadannan kananan kamfanoni na dab’i da wallafa.
GTK; Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga masu wannan sana’a musamman masu kananan kamfanoni irin naku?
Ibrahim Ibzar; Ina kira ga masu wannan sana’a su rike gaskiya da amana kuma su kara jajarcewa wajen gudanar da ayyukan wannan sana’a da fadada tunani wajen kirkiro abubuwa masu tasiri da za su amfani kasa baki daya. Akwai tarurrukan da ake shiryawa a Legas a duk shekara don baje kolin sababbin dabarun ayyukan dab’i da wallafa. Yin haka zai taimaka wajen bunkasa wannan sana’a a matakan jihohi da tarayya da kuma samun gogayya da sauran takwarorin masu wannan sana’a a ko’ina a duniya.