Daga Usman Nasidi
MAJALISAR dokokin jihar Sakkawato ta fatattaki wasu \’ya\’yanta guda biyu kan zarginsu da rashin da’a da ta yi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
\’Yan majalisar da aka sallama sun hada da Sani Yakubu da ke wakiltar al’ummar Gudu da aka sallame shi na tsawon kwanaki 40, da kuma Malami Galandanci da ke wakiltar Sakkwato ta kudu I da aka dakatar da shi na tsawon kwanaki 30.
Majalisar ta yanke shawarar sallamar su ne bayan rahoton wani kwamitin mutane 11 da aka kafa, wanda ya binciki rawar da suka taka wajen tunbuke mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar.
\’Yan majalisun su biyu sun yi ruwa sun yi tsaki wajen ganin ba a tunbuke mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar ba, inda suka ce wata hanya ce kawai don Kakakin majalisar ya kare kansa daga wata ta’asa da ya tafka.
Hakazalika majalisar ta bukaci \’ya\’yan nata guda biyu da su nemi gafarar majalisar tare da ba ta hakuri.
Sai dai da majiyarmu ta tuntubi Galadanci, sai yace “Ba zan ce komai dangane da wannan batu ba a yanzu.”