YA GARGADI GWAMNA LALONG DA YA YI HATTARA DA BATUN ZABEN KANANAN HUKUMOMI

  0
  624

  Isah Ahmed, Jos

  WANI dan kasuwa kuma shugaban kungiyar masu sayar da buhuna ta jihar Filato Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi kira ga gwamnan jihar Filato Simon Lalong kan ya yi hattara da wadanda suke kokarin ganin cewa an fitar da  karamar hukumar Jos ta arewa daga zaben kananan hukumomin jihar, da za a gudanar a watan biyu na shekara mai zuwa. Alhaji Iliyasu Muhammad ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Ya ce wannan kokari da wasu suke yi, ba  dimokuradiyya ce ta gaskiya ba, saboda an dade ba a yi zabe ba a karamar hukumar Jos ta arewa. Wanda yin hakan ya kawo wa Jihar Filato ci baya kwarai da gaske. Ya ce ya kamata a cikawa al’ummar karamar hukumar Jos alkawarin da aka yi masu,  na cewa za a gudanar masu da zaben shugabannin wannan karamar hukuma.

  Ya yi  kira ga al’ummar  karamar hukuma ta Jos ta arewa  su hada kai su ci gaba da zaman lafiyar da aka samu a wannan karamar hukuma.  Su manta da banbancin addini da kabila su zabi mutumin da ya cancanta wanda zai kawo masu ci gaba a  karamar hukumar a wannan zabe da za a gudanar.

  Daga nan ya yaba wa gwamnatin Jihar Filato kan wannan yunkuri da  take yi, na gudanar da zaben kananan hukumomin jihar. Ya ce wannan abu ne mai kyau ne wanda aka dade ana jira, domin zaben kananan hukumomi  zabe ne da yake amfanar talaka kai tsaye. Saboda shugabannin kananan hukumomi suna mu’amula da talakawa ne kai tsaye.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here