Ana Kwankwadar Kayan Kwalaben Maye Sama Da Miliyan 3 A Kano Da Jigawa Duk Rana

0
680

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

SAMA da kwalaben kayan maye Miliyan uku ne ake shanyewa a kowace rana a Jihar Kano da Jigawa

Kamar yadda bincike ya bayyana ana samun wannan matsalar ne a tsakanin mata da maza da mata, matan aure da dimbin matasa kamar yadda \’yan majalisar dattawa suka gabatar a gaban majalisar a jiya.

Dan Majalisar Dattawa Sanata Baba Kaka Bashi Garbai ne ya gabatar da kudurin,  Sanatan wanda yake wakiltar mutanen Jihar Borno ya samu amince wa \’yan majalisar da dama duk sun bayyana cewa akwai bukatar a binciki ayyukan wuraren sayar da magunguna sakamakon irin bunkasar da ake samu a kan lamarin shan kayan maye tsakanin mata da matasan kasa baki daya.

Kudirin ya samu amincewar Sanata Jibril Barau APC daga Jihar Kano. Garbai ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa ana shanye kwalaben kayan maye a jihohin Kano da Jigawa da suka kai Miliyan 3 zuwa 8 a kowace rana.

Alkalumman sun yi bayanin cewa ko a batun matsalar \’yan Boko Haram ma batun na shaye-shaye ya taka rawa kwarai.

Kodayake Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana cewa lamarin ba wai na arewacin Nijeriya kadai ba ne, don haka lamari ne da za a dauke shi na kasa baki daya.

Kamar yadda wakilinmu ya binciko lamarin shaye-shaye tsakanin mata ya yi tsamari kwarai domin ya zamar wa manyan mata da matasa tamkar dole saboda halin kuncin da tsananin tunanin da suke tsintar kansu a ciki.

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here