Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABAN kungiyar Direbobin Tanka na kasa reshen Jihar Kaduna PTD Kwamared Abdulraheem Haruna 63 ya bayyana gamsuwarsa dangane da matakin da gwamnatin Jihar Kaduna ta dauka na gyara wurin da manyan motocin daukar mai za su tsaya a garin Tafa da Marabar Jos.
Shugaban ya kuma bayyana cewa gyaran wurin zai taimaka wajen rage cunkuson manyan motoci wanda haka kuma zai taimaka wajen kare rayukan Jama’a.
Kwamared Haruna 63 ya jajanta wa mutanan da suka rasa rayukansu yayin hadarin da ya faru a karshen mako a garin Tafa yayin da wata Tanka ta kone dauke da man fetur.
A kan hakan, shugaban ya bukaci daukacin ‘ya’yan kungiyar na PTD da su ci gaba da bin dokokin kasa da kuma bin ka’idar tuki.