Sun Kubutar Da Wadda Aka Sace Lami-Lafiya

0
817

MUSA MUHAMMAD KUTAMA,  Daga Kalaba

RUNDUNAR ‘yan sandan Jihar Kuros Riba ta yi katari wajen kubutar da Uwargida Comfort Bassey Udoenwang,da ke layin Jesus karamar hukumar Kalaba ta kudu,  daga hannun wasu da ake zargi masu kama mutane suna yin garkuwa da su domin karbar kudin fansa, suka boyeta a kauyen Akpap Okoyong ,karamar hukumar Odukpani  bayan wani samame da jami’an sashen da ke yaki da masu kama mutane suna garkuwa da su da kuma masu aikata sauran nau’in tsageranci na rundunar suka kai a makon nan da muke ciki.

Da yake yi wa wakilinmu na kudanci karin bayani yadda aka yi har nasarar ta samu Hafiz Muhammad Inuwa,kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ci gaba da cewa “ yadda aka yi ma har waccan nasara ta samu shi ne jami’anmu ne aka kyankyasawa maboyar kuma ba su yi kasa a gwiwa ba suka garzaya sukayi sa’ar kubutar da matar bayan barin wuta da aka yi tsakanin ‘yan sandanmu da wadanda suka yi garkuwa daga ciki ma an kashe daya daga cikinsu sauran sun arce da  raunuka  jikinsu da suka samu a musayar wutar “.inji shi.

Ya ci gaba da cewa  “lokacin da masu laifin suka ga ‘yan sanda sun tunkari maboyar su sai suka bude musu wuta amma duk da haka sun yi ta maza daya daga cikin masu garkuwa da mutanen mai suna Isaac Sabastine,  dan asalin karamar hukumar Obot Akara, jihar Akwa Ibom da aka raunata sanadiyar musayar wutar ya arce da raunuka jikinsa”.An kama wani mai suna Elele David, shi kuma jagoran masu garkuwar Ayi Etok ya arce da  raunuka da ya samu sanadin musayar wutar da ‘yan sanda.

Kayayyakin ta’addanci da aka samu wurin su sun hada da bindiga kirar gida babba da kuma karama, kayan ‘yan sanda da kuma tsumman da suke rufe wa wanda suka kama fuska, kana kuma an gano wata mota kirar Toyota mai lamba ANA420 CK.Gawar wanda aka kashe a musayar wutar na asibitin koyaswa na jami’ar Kalaba yayin da matar da aka kubutar tare da kayayyakinta lokacin da suka sace ta an ba ta an kuma  sada ta da iyalanta.

Daga nan kwamishinan ‘yan sandan ya kara jaddada aniyarsa ta gain rundunarsa ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba na kakkabe bata-gari da zarar an shaida mata ta kuma ci gaba da bayar da tsaro bakin gwargwado ta yadda kowane mazaunin Kuros Riba zai rika yin barci da saleba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here